Tsadar Rayuwa: Ganduje Ya Kaddamar da Shirin Tallafawa Matasa 484 a Kano
- Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da wani shirin ba da tallafi ga matasa maza da mata a jihar Kano
- Abdullahi Ganduje ya ce tallafin wata biyayya ce ga kiran da Shugaba Bola Tinubu ya yi ga masu rike da mukaman siyasa a fadin kasar nan
- Wanda ya ba da tallafin, Nasiru Ja’oji wanda jigon jam'iyyar APC ne a Kano ya ce matasa 484 sun amfana da kyautar kudi da kayan sana'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya kaddamar da shirin tallafawa matasan jihar Kano 484 da suka hada da maza da mata.
An rahoto cewa maza da matan da suka samu rabauta da shiga shirin sun samu tallafin kudi, injin dinki da kuma babura.
Ganduje ya kaddamar da shirin tallafi
Jaridar Leadership ta rahoto cewa Abdullahi Ganduje ya samu wakilcin Mukhtar Adamu, shugaban ma'aikatansa a wajen kaddamar da rabon tallafin.
Shugaban jam'iyyar na kasa, Ganduje ya nuna godiya ga Nasiru Ja’oji bisa yadda ya karfafa matasa da mata a jihar Kano.
"Wannan zai kasance a matsayin biyayya ga kiran da Shugaba Bola Tinubu ya yi ga masu rike da mukaman siyasa da su bullo da dabarun magance matsalolin tattalin arziki."
- A cewar Abdullahi Ganduje.
Ja’oji ya tallafawa matasan Kano
A nasa jawabin, jigo a APC daga Nasarawa a Kano, Nasiru Ja’oji ya bayyana tallafin a matsayin wani kokarinsa na tallafawa matasa kasancewarsa mai rike da mukamin siyasa.
Nasiru Ja'oji ya ce an zakulo matasa 484 da za su ci gajiyar shirin ne bisa cancanta inda ya ce mutane hudu za su samu tallafin Naira miliyan daya kowannensu.
"Za mu rabawa mutane 200 talalfin N200,000 kowannensu yayin da mutane 100 za su samu tallafin N50,000 kowannensu.
“Hakazalika, a taron na yau, za a ba mutane 100 tallafin jimillar N20,000 kowanne, yayin da mutane 50 za su tafi gida da injinan dinki sannan kuma za a ba mutane 30 tallafin babura."
- A cewar Nasiru Ja’oji.
A madadin wadanda suka ci gajiyar shirin, Abdullahi Musa, wanda aka ba babur, ya bayyana godiyarsu ga Ja’oji, tare da yin kira ga sauran masu hannu da shuni da su yi koyi da shi.
Ganduje ya ba ta tallafin N115m
A wani labarin, mun ruwaito cewa Abdullahi Umar Ganduje ya kara tallafawa mazauna Kano da Naira miliyan 115 domin rage radadin da suke ciki.
An rahoto cewa wannan tallafin ya ba kwamitin raba kayan rage radadi wanda Farfesa Yahuza Bello ke jagoranta damar sanya farin ciki ga gidaje 50,000 a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng