Kano: Ganduje ya kaddamar da rabon tallafin abinci ga mabukata (Hotuna)

Kano: Ganduje ya kaddamar da rabon tallafin abinci ga mabukata (Hotuna)

A cikin kokarin rage zafi ga jama'ar da aka kulle duk da za a fara azumin watan Ramadan mai alfarma, Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya kaddamar da fara raba tallafi ga jama'a mabukata na jihar Kano.

An kaddamar da fara raba tallafin ne a wurin ajiye kayayyaki da ke Bompai a jihar Kano.

Wurin ya samu halartar mambobin kwamitin tara kudin tallafi na jihar, karkashin shugabancin Farfesa Muhammad Yahuza Bello da mataimakinsa Tajudeen Aminu Dantata.

Kano: Ganduje ya kaddamar da rabon tallafin abinci ga mabukata (Hotuna)

Kano: Ganduje ya kaddamar da rabon tallafin abinci ga mabukata (Hotuna)
Source: Twitter

"Wannan babban al'amari ne da ke tunkaro mu a yayin fuskantar kalubalen annobar Coronavirus.

Yanzu kusan makonni uku kenan da muka rufe iyakokin jihar nan.

A yayin da muke kokarin kare rayuka, dole ne mu nemi hanyar tallafawa masu karamin karfi a jihar nan," gwamnan yace.

Kano: Ganduje ya kaddamar da rabon tallafin abinci ga mabukata (Hotuna)

Kano: Ganduje ya kaddamar da rabon tallafin abinci ga mabukata (Hotuna)
Source: Twitter

A kokarin raba kayan tallafin da suka hada da garin tuwo, taliya, indomie, man girki da sauran kayan abinci, kwamitin tattara kudin tallafin ya ce zai bi tsarin akwatin zabe ne wajen raba kayayyakin.

Farfesa Bello, wanda shine shugaban kwamitin, ya ce za a fara rabawa ne a kananan hukumomi 8 da ke tsakiyar birnin Kano.

Kano: Ganduje ya kaddamar da rabon tallafin abinci ga mabukata (Hotuna)

Kano: Ganduje ya kaddamar da rabon tallafin abinci ga mabukata (Hotuna)
Source: Twitter

Sun hada da Nasarawa, Dala, Gwale, Kumbotso, Fagge, Tarauni, Ungogo da birnin Kano.

Ya ce a kowacce karamar hukumar, sun tantance yawan mabukatan da za su baiwa tallafin.

Ya kara da cewa, "A karamar hukumar Nasarawa, akwai mabukata 3,122, Dala akwai mabukata 2,672, a Gwale akwai mabukata 1,800, a Kumbotso akwai mabukata 1,633.

"A Fagge akwai mabukata 2,084, a Tarauni akwai mabukata 1,606, a Ungogo akwai mabukata 1,536 sai kuma birnin Kano da ke da 2,524."

Kano: Ganduje ya kaddamar da rabon tallafin abinci ga mabukata (Hotuna)

Kano: Ganduje ya kaddamar da rabon tallafin abinci ga mabukata (Hotuna)
Source: Twitter

Gwamna Ganduje ya yi kira ga mabukatan da su bi tsari wajen karban kayayyakin ba tare da cin zarafi don wulakanci ga masu rabawar ba, wadanda za su hada da sarakunan gargajiya da sauran shugabannin al'umma.

Kano: Ganduje ya kaddamar da rabon tallafin abinci ga mabukata (Hotuna)

Kano: Ganduje ya kaddamar da rabon tallafin abinci ga mabukata (Hotuna)
Source: Twitter

"Ina kira ga jama'a da su kiyaye dukkan dokokin da masana kiwon lafiya suka bayyana. Wanke hannu akai-akai da sabulu a karkashin ruwa mai gudana da amfani da sanitiser na da matukar amfani.

Kano: Ganduje ya kaddamar da rabon tallafin abinci ga mabukata (Hotuna)

Kano: Ganduje ya kaddamar da rabon tallafin abinci ga mabukata (Hotuna)
Source: Twitter

"A yi kokarin kiyaye dokar nisantar juna a kowanne lokaci. Ina kira ga jama'a da su mutunta dokar hana zirga-zirga a jihar," gwamnan yace.

Kano: Ganduje ya kaddamar da rabon tallafin abinci ga mabukata (Hotuna)

Kano: Ganduje ya kaddamar da rabon tallafin abinci ga mabukata (Hotuna)
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel