A karo na biyu: Ganduje ya bada tallafi don rage wa jama'ar Kano radadi
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kara tallafa wa kwamitin raba kayan rage radadi wanda Farfesa Yahuza Bello ke jagoranta da miliyan 115 don su sake raba wasu kayayyakin a jihar.
A yayin zantawa da manema labarai a kan ayyukan kwamitin, Bello, wanda shine shugaban jami'ar Bayero da ke Kano, ya ce a karon farko na rabon, an mika tallafi ga gidaje 50,000 a jihar.
Ya ce kwamitin ya yi niyyar mika tallafin ga gidaje 300,000 da ke jihar amma 50,000 suka samu a karo na farko. A yanzu za su kara bai wa wasu gidaje 50,000 tallafin har sai sun cike 300,000.
Amma kuma shugaban ya musanta zargin da hukumar yaki da rashawa ta jihar ke yi wa shugaban karamar hukumar Kumbotso.
Ya ce babu wani waskar da kayan tallafin da yayi don ba kayan aka basu suna rabawa ba, fom ne kadai.
Laifin shugaban karamar hukumar shine bai wa wadanda basu dace ba fom din da yayi.
Bello ya ce abinda shugaban hukumar yaki da rashawa na jihar ya kamata yayi shine, ya rubuta wasika ga kwamitin tare da bukatar bayani a kan lamarin amma ba wai ya kai kotu ba.
KU KARANTA: Kashe-kashen 'yan bindiga: Yadda dan majalisa ya fashe da kuka a yayin zaman majalisa
A wani labari na daban, mataimakin kakakin majalisar jihar Katsina, Shehu Tafoki ya samu damar yi wa zauren majalisa jawabi amma sai ya fashe da kuka a kan rashin tsaron da ya addabi mazabar Faskari.
Yankunan sun saba samun hare-haren 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da duk wani nau'in rashin tsaro.
A makon da ya gabata, mutum biyar suka halaka sakamakon hare-haren da aka kai a kananan hukumomin Faskari da Sabuwa.
Tafoki, wanda ke wakiltar mazabar Faskari a majalisar jihar, ya ce ba a samun rana daya a halin yanzu da za ta wuce ba tare da an ji harin da aka kai yankin ba.
Kamar yadda yace, karamar hukumar Faskari a halin yanzu za a iya kwatanta ta da Maiduguri, "Ko a daren jiya 'yan bindiga sun kai hari garin Daudawa inda suka yi garkuwa da mutum 4 sannan suka raunata wasu."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng