Uwargidan Gwamna Ta Ji Tausayin Talakawa, Ta Raba Tallafin Kudi ga Mata 1575

Uwargidan Gwamna Ta Ji Tausayin Talakawa, Ta Raba Tallafin Kudi ga Mata 1575

  • Uwargidan gwamnan Imo, Misis Chioma Uzodimma ta ba mata 1,575 tallafin kudi da kayan noma a shirinta na bunkasa rayuwar matan jihar
  • Misis Chioma Uzodimma ta bayyana cewa shirin tallafawa mata 1,575 wata alama ce ta jajurcewarta na samar da damarmaki ga kowa
  • Daga cikin tallafin da ta bayar akwai tallafin N50,000 ga kowace karamar 'yar kasuwa a yankunan karkara, da irin noma ga mata 1,000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Imo - Uwargidan gwamnan Imo, Misis Chioma Uzodimma, ta sake bunkasa rayuwar mata a jihar ta hanyar sanar da ba da tallafi ga mata 1,575.

Uwargidan gwamnan ta sanar da ba da tallafin ne filin taro na Rear Admiral Ndubuisi Kanu da ke Owerri a lokacin rufe babban taron matan Imo na Agustan 2024.

Kara karanta wannan

Bayan ambaliya ta kashe mutum 37, gwamnati ta ba da umarni kan madatsar Alau

Uwargidan gwamnan Imo ta yi magana kan muhimmancin bunkasa mata
Uwargidan gwamnan Imo, Misis Chioma Uzodimma ta ba mata 1575 tallafi. Hoto: @Hope_Uzodimma1
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta ruwaito Misis Chioma Uzodimma ta sanar da cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A yau mun dauki muhimmin mataki na ci gaba ta hanyar tallafawa mata 1,575 a bangarori daban-daban tare da nuna jajircewarmu na samar da damarmaki ga kowa."

Uwargidan gwamna ta tallafawa mata

Shirye-shiryen sun haɗa da: Tallafawa kanana da matsakaitan 'yan kasuwa 135 a karkara da manyan birane da tallafawa ƙungiyoyin noma 1000 a cikin yankunan karkara.

Sauran sun hada da ba da tallafin noma ta hanyar raba irin rogo, dankali, da masara, tare da tsabar kudi N50,000 ga manoman karkara 1,000

Shirin karshe shi ne ba da tallafin N50,000 ga kowace karamar 'yar kasuwa a yankunan karkara, wanda ya kunshi unguwannin 305, inji rahoton The Guardian.

Uwargidan gwamna ta karfafi mata

Uwargidan gwamnan ta jaddada cewa:

"Sanin tarihinmu ya na da mahimmanci domin tafiyar da makomarmu cikin dabara.

Kara karanta wannan

Ambaliyar Borno: Gwamna a Arewa ya ba Zulum tallafin N50m da jirage 6

""Nwanyị DịIke kalma ce da ke nuna macen zamani wacce ke daidaita tarin ayyukanta yayin da ta ke fuskantar ƙalubale tare da shawo kan matsalolinta.:

Misis Uzodimma ta bukaci mata da su yi amfani da karfin zuciyarsu su tsaya tsayin daka wajen fuskantar kalubale da kuma yin jagoranci cikin kwarin gwiwa.

Uzodimma ya yiwa matarsa kalamai

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya taya matarsa murna yayin da take bikin murnar kara shekara.

Gwamnan wanda ya tsinci kansa cikin tunawa da soyayyar da ke tsakaninsu, ya bayyana matarsa, Chioma Uzodimma, da hasken da ta haskaka rayuwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.