Hotunan auren diyar gwamna sun kayatar, kalaman matar gwamna sun narka zuciya

Hotunan auren diyar gwamna sun kayatar, kalaman matar gwamna sun narka zuciya

  • Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya aurar da diyarsa, Oprah Chioma Uzodinma a wani bikin gargajiya da aka yi a Abuja
  • A wallafar da uwargidan gwamnan, Chioma Uzodinma ta yi a shafinta na Instagram, ta saka hotunan amaryar da ango cike da annashuwa
  • Ta yi wa ma'auratan fatan alheri tare da zaman lafiya cike da wadata, kwanciyar hankali da kaunar juna a zaman da za su yi

FCT, Abuja - Oprah Chioma Uzodimma, diyar Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ta auri rabin ranta, Henry Ohaeri.

Sabuwar amaryar da angonta sun yi bikin gargajiyansu a Federal Marriage Registry a Abuja.

Uzodinma da matarsa Chioma sun samu damar hallartar bikin inda suka bayyana cike da farin ciki da annashuwa.

Kara karanta wannan

Ka yi abin kirki: Gwamnan PDP ya yabi Buhari kan yafewa Joshua Dariye da Jolly Nyame

Kyawawan hotunan auren diyar Gwamna Hope Uzodinma sun kayatar
Kyawawan hotunan auren diyar Gwamna Hope Uzodinma sun kayatar. Hoto daga @he_chiomauzodinma
Asali: Instagram

A wallafar da Mai girma uwargidan gwamnan Imo ta yi a shafinta na Instagram, ta bayyana wasu kalamai masu matukar taba zukata a matsayinta na mahaifiyar amaryar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ga kalaman mahaifiyar amaryar:

"A cikin shekaru da yawa, na ga kyakkyawar ’yarmu, Oprah Chioma Uzodimma da hasken zuciyarta, Henry Ohaeri, sun ba da damar soyayya ta rikide tare da shiga mutanen kirki. Don haka kallon da na musu suna furta alwashi jiya a wurin rajistar aure na tarayya, Abuja ya sanya ni alfahari.
"Labarun soyayya suna da kyau, amma samun damar shaida girma, sadaukarwa, da haɗin kan wannan soyayyar tsakanin danginku da wani, jin daɗi ne na daban da ba za ku taɓa kwatantawa ba."

Ta kara da cewa:

"Iyalan Ohaeri da Uzodimma sun yi wani gagarumin biki na bikin auren 'ya'yansu a kotu kuma muna da kwarin gwiwar cewa tare, sabbin ma'auratan za su iya fuskantar duk wata guguwa, ko ta yaya za ta iya tasowa.

Kara karanta wannan

Hasashe mai daukar hankali: Musulmai za su azumci Ramadana sau biyu a 2030

"Har ila yau, a wannan rana mai farin ciki, ina taya ma'auratan mu masu ban sha'awa, Mista da Mrs. Henry Ohaeri, kuma ina yi musu addu'a kan tafarkin da ke gabansu a cikin rayuwar aurensu ta kasance cikin nasara, kwanciyar hankali, da wadata. Amin.
"Barr. (Mrs.) Chioma Uzodimma.Uwargidan shugaban kasa, jihar Imo, kuma wacce ta kafa gidauniyar GoodHope Flourish."

Hotunan kyawawan 'yan 3 da ke soyayya da saurayi 1, sun ce suna shirin aurensa

A wani labari na daban, yayin da auren mutum daya da 'yan biyu masu kama daya yazo wa mutane da dama a abin al'ajabi, 'yan uku daga Kenya na shirin rayuwa da miji daya.

Labarin Eve, Mary da Cate na da ban sha'awa. Suna matukar kama da juna, sannan wani abun burgewa, suna da ra'ayi daya.

'Yan ukun masu kama da juna sun bayyana yadda suke soyayya da mutum daya, wanda ya fada tarkon soyayyarsu a wurare daban-daban.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da ya kamata ka sani game shugaban cibiyar Kididdigan Najeriya da ya mutu yau

Asali: Legit.ng

Online view pixel