Bayan Shekaru, Gwamna Abba Ya Sakawa Yarinyar da Taimaka Masa a Zaben 2019

Bayan Shekaru, Gwamna Abba Ya Sakawa Yarinyar da Taimaka Masa a Zaben 2019

  • Abba Kabir Yusuf ya fara maida alherin da wasu magoya baya da masoya su ka yi masa tun kafin ya zama gwamna
  • Gwamnan Kano ya aika kudi zuwa ga wata yarinya wanda ta fasa asusunta domin ba shi gudumuwa a zaben 2019
  • Hotuna sun nuna irinsu AGY Yakasai sun tashi da kyautar sabon babur da kudi domin ya samu saukin radadin rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - A lokacin zaben 2019, Abba Kabir Yusuf ya nemi takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar adawa ta PDP.

Idan za a iya tunawa, hukumar INEC ta tabbatar da Abdullahi Umar Ganduje da APC ne su ka yi nasara bayan kai ruwa rana.

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa na neman muƙamin mataimaki a 2027? ya yi magana

Abba Gida Gida
Abba Gida Gida ya aikawa budurwa sako a Kano Hoto: Salisu Yahaya Hotoro
Asali: Facebook

Yarinyar da ta fasa asusu domin Abba

Lokacin da Abba Kabir Yusuf ya nemi kujerar zama gwamna, wata yarinya ta taimaka masa da gudumuwa daga asusunta.

Shekaru fiye da biyar da wannan abin ya faru, sai aka ji labari cewa Mai girma Abba Kabir Yusuf ya tuna da wannan masoyiyar.

Salisu Yahaya Hotoro wanda ya na cikin hadiman gwamnan Kano ya nuna hotuna a Facebook da ke nuna an aika mata kyauta.

Bisa dukkan alamu kudi ne aka kunsa a cikin ambula aka tura mata a matsayin sakayyar fasa asusun da ta yi domin shi a 2019.

Salisu Hotoro ya rubuta:

“Ita ma wannan yarinyar ai za ku iya tuna ta ko? Ita ce a shekarar 2019 ta bai wa Abba Gida-Gida asusunta wanda ta dade tana tara kudi a matsayin gudummawar takararsa.

Kara karanta wannan

Yunwa: Wasu Gwamnonin jihohin Kudu sun fitar da tsarin wadata jama'a da abinci

Ita ma yau mai girma gwamna ya sanya ta cikin alkairi dumu-dumu.”

Gwamna Abba ya tuna da 'yar makaranta

Kafin nan an ji labarin yadda gwamnan na Kano ya aika da irin wannan kyauta a cikin ambula ga wata budurwa mai kaunarsa.

Salisu Hotoro ya fitar da hotunan yarinyar inda aka gan ta sanye da riga mai dauke da sunan Abba lokacin ta na makarantar sakandare.

Malam Hotoro ya rubuta cewa Mai girma gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf yau ya sanya ta cikin alkairi dumu-dumu.

"Daga ina Abba yake rabon kudin?"

Ganin kyauttukan da Abba yake yi, wasu sun fara tambaya ko dukiyar al’umma ake tabawa ko kuwa daga albashinsa na gwamna ne.

Su kuwa wasu samarin abin da suke fada shi ne a ba su lambobin wayar ‘yan matan.

Wasu sun gaji da tafiyar Abba da NNPP

Rahoto ya zo cewa wasu su na ta barin tafiyar Kwankwasiyya, irinsu Ali Jita sun komawa jam'iyyar APC ne mai mulki a Najeriya.

A ‘yan kwanakin nan an ga gwamnan jihar Kano ya raba motoci da babura ga masoyansa a ciki har da ‘yan wasan kwaikwayo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng