Kai tsaye: Yadda zaben jihar Kano ya gudana - INEC

Kai tsaye: Yadda zaben jihar Kano ya gudana - INEC

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC, ta kaddamar tare da shellanta nasarar Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyyar APC, gwamnan jihar Kano da ya sake lashe zaben jihar karo na biyu da aka gudanar a ranar Asabar.

Biyo bayan kammala zaben cike gurbi da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Maris, hukumar INEC ta tabbatar da nasarar gwamna Abdullahi Umar Ganduje a matsayin zababben gwamnan jihar Kano karo na biyu.

Yayin shellanta wanda ya yi nasara a zaben, babban Baturen zabe na jihar Kano, Farfesa Bello Shehu, ya ce Ganduje ya yi nasara da gamayyar kuri'u 1,033,695 inda ya lallasa abokin adawar sa na jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf wanda ya lashe kuri'u 1,024,713.

Shugaban hukumar INEC na kasa; Farfesa Mahmood Yakubu
Shugaban hukumar INEC na kasa; Farfesa Mahmood Yakubu
Asali: Twitter

Ba ya ga cika duk wasu sharudda da tanadi na dokar hukumar zabe da kuma kundin tsarin mulkin kasar nan, Farfesa Shehu ya ce dan takara na jam'iyyar APC ya lallasa abokin adawar sa na jam'iyyar PDP da tazara ta kimanin kuri'u 8,982.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, gwamna Ganduje ya yi nasara bayan maimacin zabe da aka gudanar cikin kananan hukumomi 28 da ke fadin jihar Kano biyo bayan takkadama ta soke zabukan wasu yankuna yayin zaben da aka gudanar a ranar Asabar 9, ga watan Maris da hukumar INEC ta kaddamar da hukunci cewa bai kammala ba.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, bayan da dan takara na jam'iyyar APC ya samu gamayyar kuri'u ta 987,819, dan takara na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 1,014,474 yayin zaben da aka gudanar makonni biyu da suka gabata.

A yayin zaben cike gurbi da hukumar INEC ta gudanar a ranar Asabar, gwamna Ganduje da ya kasance dan takara na jam'iyyar APC, ya samu kuri'u 45,876 yayin da Abba Yusuf na jam'iyyar PDP, ya tashi da kuri'u 10,239 kacal.

KARANTA KUMA: Zaben cike gurbi: Nasarar Ganduje ta haifar da dimuwa a jihar Kano

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Kano, Alhaji Rabi'u Suleiman Bichi, ya hau kujerar naki ta rashin amincewa da sakamakon zaben cike gurbi da hukumar INEC ta gudanar musamman na unguwar Gama da ke karamar hukumar Nasarawa.

Ba ya ga rashin amincewa da rattaba hannu kan sakamakon zaben, shugaban jam'iyyar PDP ya yi kira ga hukumar INEC da ta yi gaggawar soke zaben da a cewar sa ba ya da wata nasaba ta kusa ko ta nesa da inganci ko kuma gaskiya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel