‘Tun 1999’: An Yi Shekara 25 a Jiha ba Tare da An Dauki Ma’aikatan Gwamnati ba

‘Tun 1999’: An Yi Shekara 25 a Jiha ba Tare da An Dauki Ma’aikatan Gwamnati ba

  • Mutane su na ta murna a jihar Kuros Riba wannan karo domin za a rage adadin masu zaman kasha wando
  • Gwamna Bassey Otu ya yarda a dauki ma’aikata bayan an shafe shekaru sama da 20 ba a ga haka a jihar ba
  • Kwamishinan yada labarai na Kuros Riba ya shaida cewa a tashin farko za dauki mutane 2, 000 aiki a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Cross River - Sai a kwanan nan aka ji cewa gwamnatin Kuros Riba ta cire dogon takunkumin da ta maka na hana daukar aiki.

An shafe shekaru 25 rabon da a bude kofar daukar ma’aikatan gwamnatin a jihar Kuros Riba duk da yadda matasa ke neman abin yi.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game manyan ƴan takara 3

Gwamna Bassey Otu
Gwamna Gwamna Bassey Otu ya amince a dauki ma’aikata aiki a gwamnatin Kuros Ribas Hoto: @officialspbo
Asali: Twitter

Gwamna ya yi na'am da daukar aiki

Punch ta rahoto cewa Mai girma Bassey Otu ya cire wannan takunkumi na daukar mutanen da za su yi wa gwamnatin jihar aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan yada labarai na Kuros Riba, Erasmus Ekpang ya shaidawa ‘yan jarida haka watanni bayan an dauki malamai aiki.

Dr. Erasmus Ekpang ya bayyana wannan ne a lokacin da ya zanta da manema labarai kamar yadda hukumar dillacin labarai ta rahoto.

Kwamishinan yake cewa rabon da a bude kofar daukar ma’aikatan gwamnati a Kuros Riba tun 1999, shekaru kimanin 25 kenan.

Ma'aikatan gwamnati nawa za a dauka aiki?

A zagayen farko na ma’aikatan da za a dauka wannan karo, za a zakulo mutane 2, 000.

Lokacin da yake jawabi a garin Kalaba, Erasmus Ekpang ya yi alkawarin za a fara daukar aikin ne nan take ba tare da an bata lokaci ba.

Kara karanta wannan

Sabon albashi: Gwamnan Kano ya fadi lokacin da zai fara biyan ma'aikata N70000

Za a dauki ma’aikata a duka ma’aikatu, hukumomi da kuma cibiyoyin gwamnatin Kuros Riba a karkashin jagorancin Sanata Bassey Otu.

Tsohon gwamna ya so ya dauki ma'aikata

Rahoton Premium Times ya ce an yi yunkurin daukar sababbin ma’aikata a lokacin mulkin Ben Ayade, amma gwamnati mai-ci ta soke shirin.

Kamar yadda aka saba gani bayan an yi canjin gwamnati, sabuwar gwamnatin Kuros Riba ta ce an saba ka’ida wajen shirin daukar ma’aikata.

Kwamishinan ya koka da cewa ana fama da karancin ma’aikata a yanzu, ya kuma ce daga baya za a yi batun kara albashi zuwa N70, 000.

Bashin kasashe a bankin duniya

A wani rahoto, an fahimci ana bin Najeriya makudan kudi da ya kai N27tr a bankin duniya saboda bashi da gwamnatin kasar ta rika ci.

Bangladesh da Fakistan ne kurum a yau suka fi Najeriya bashi mai nauyi a bankin da ke Amurka kamar yadda alkaluma suka nuna a yau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng