"Zai Yi Wahala," NNPP Ta Yi Martani kan Samun 'Yan Kwaya a cikin 'Yan Takararta

"Zai Yi Wahala," NNPP Ta Yi Martani kan Samun 'Yan Kwaya a cikin 'Yan Takararta

  • Jam'iyyar NNPP ta yi martani kan labarin samun yan takara akalla 20 da ta'ammali da miyagun kwayoyi bayan gwaje-gwaje
  • Hukumar zaben jihar (KANSIEC) da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) sun hada kai wajen gwada yan takarar
  • A zantawarsa da Legit, shugaban NNPP reshen jihar Kano, Hashim Dungurawa ya bayyana cewa babu 'yan kwaya a tafiyar Kwankwasiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Jam'iyyar NNPP reshen jihar Kano ta barranta yan takararta a zaben kananan hukumomi mai zuwa da amfani da miyagun kwayoyi.

An samu rahoto a safiyar Laraba da ke zargin wasu 'yan takara 20 da amfani da miyagun kwayoyi ciki har da kodin da hodar iblis, lamarin da NNPP ta ce sai dai tuntuben na'urar NDLEA kawai.

Kara karanta wannan

NNPP ta fito da mace a matsayin 'yar takarar shugaban karamar hukumar Kano

Dungurawa
NNPP ta ce babu 'yan kwaya a cikinta Hoto: Mustapha Kakisu Yalwa
Asali: Facebook

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa a martaninsa, shugaban NNPP na Kano, Hashim Dungurawa ya bayyana cewa zai yi wahala sosai a samu yan kwaya a cikinsu.

Jam'iyyar NNPP ta fadi irin yan takararta

Shugaban NNPP reshen jihar Kano, Hon. Hashimu Dungurawa ya shaidawa Legit Hausa cewa dukkanin yan takararta nagartattu ne, masu ilimi.

Ya bayyana cewa jam'iyyarsu ba ta ba 'yan kwaya ballantana har ta kai ga ba su takarar shugabantar jama'a.

NNPP ta fayyace tsarin Kwankwasiyya

Jam'iyyar NNPP a Kano ta ce tsarin Kwankwasiyya na tafiya ne a doron samar da ci gaba da ilimantar da matasa domin samun rayuwa mai inganci.

Dr. Hashim Dungurawa da ya bayyana haka a Kano ya kara da cewa duk wanda ya san Kwankwasiyya, ya san kullum fafutuka ta ke kan ilimantar da jama'a.

Kara karanta wannan

'Yan takarar NNPP 20 na ta'ammali da kwayoyi a kano? NDLEA ta yi karin haske

Zabe: Gwamnatin NNPP ta shirya gwajin kwaya

A baya mun ruwaito cewa gwamnatin NNPP da ke jagorantar jihar Kano ta shirya gudanar da gwajin ta'ammali da miyagun kwayoyi ga yan takara a zaben kananan hukumomi.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Kano, Farfesa Sani Malumfashi da ya bayyana haka ya kara da cewa, za a gwada yan takarar shugaban kananan hukumomi da kansiloli a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.