Rarara Ya Sake Shirya Abin Alheri, Zai Ginawa 'Yan Jihar Kano Titi

Rarara Ya Sake Shirya Abin Alheri, Zai Ginawa 'Yan Jihar Kano Titi

  • Fitaccen mawakin siyasa, Dauda Abdullahi Kahutu Rarara ya kaddamar da shirin gina titi a jihar Kano
  • Mawakin ya bayyana damuwa kan yadda mutanen yankin Darmanawa ke shan wahala saboda matsalar hanyar
  • Aikin hanyar zai fara ne daga Darmanawa zuwa Gandun Sarki domin saukakawa al'ummar yankin a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Fitaccen mawakin siyasa a Arewacin Najeriya, Dauda Kahutu Rarara zai yi wa yan jihar Kano abin alheri.

Mawakin ya kaddamar da aikin gina sabon titi daga ofishin yan sanda na Darmanawa zuwa Gandun Sarki.

Dauda Kahutu Rarara zai gina titi a Kano
Mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara zai gina titi a Kano domin saukakawa al'umma. Hoto: Rabi'u Garba Gaya.
Asali: Facebook

Kano: Rarara ya kaddamar da aikin titi

Hadimin mawakin, Rabiu Garba Gaya shi ya tabbatar da haka a shafinsa na Facebook a yau Laraba 11 ga watan Satumbar 2024.

Kara karanta wannan

"Za mu kai dauki Maiduguri": Tinubu ya aika sako ga Zulum bayan ambaliyar ruwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rarara ya ce ya ba da umarnin fara aikin hanyar saboda abubuwa da ke faruwa a hanyar da ke yankin ya yi yawa.

Mai unguwar Darmanawa ya yi godiya ga mawakin inda ya tabbatar masa irin wahalar da suke sha saboda rashin kyawun hanyar.

Ya ce mata da yawa sun samu matsala har cikinsu ya zube saboda matsalar hanyar ta Darmanawa.

Kalubale da Rarara ke fuskanta a Arewa

Wannan aikin na titi da Rarara ya kaddamar na zuwa ne yayin da ya ke shan suka kan layin siyasarsa ta goyon bayan Bola Tinubu musamman a Arewacin Najeriya.

Rarara ya cigaba da nuna goyon baya ga shugaban wanda ya fusata yan Arewacin kasar da suke ganin ya watsa musu kasa a ido.

Hakan ya saka mutane da dama da ke da daga rakiyar mawakin inda suke cewa ya cika butulu duk da halin da Arewa ke ciki.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisa ya koka da sace mutane a asibitin Kaduna, ya fadi abin da ake bukata

Rarara zai gina tituna 7 a Katsina

Kun ji cewa fitaccen mawaki Dauda Kahutu Rarara ya bayyana ba da ayyukan gina tituna a yankuna daban-daban na jihar Katsina a Arewa maso Yamma.

An ruwaito cewa, za a yi titunan ne guda bakwai a wasu yankunan da aka bayyana a kananan hukumomin jihar.

Jama’a sun yi martani, sun yi addu’ar Allah ya saka ga Rarara da kuma yi masa fatan alheri a rayuwarsa da aikinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.