'Yan Bindigar da Suka Sace Dan Siyasa a Arewa Sun Turo Sako, Sun Fadi Bukatunsu
- 'Yan bindigar da suka sace Japheth Zarma Yakubu, wani mai neman takarar kansila a Kaduna sun bukaci Naira miliyan 20 kudin fansa
- An rahoto cewa 'yan bindigar sun kira iyalan dan siyasar da ke zaune a gundumar Kurmin-Kare, karamar hukumar Kachia kan bukatunsu
- Baya ga Naira miliyan 20, an ce 'yan bindigar sun bukaci iyalan su kai masu sababbin babura biyu ma damar sun so a sako Japheth Yakubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - 'Yan bindigar da suka yi garkuwa da wani mai neman takarar kansila a gundumar Kurmin-Kare da ke karamar hukumar Kachia ta jihar Kaduna, sun aiko sako.
An rahoto cewa 'yan bindigar sun bukaci Naira miliyan 20 da kuma babura biyu matsayin kudin fansa kafin su sako dan siyasar mai suna, Japheth Zarma Yakubu.
'Yan bindiga sun nemi N20m
Wani shugaban yankin wanda ya bayyana hakan ga jaridar Daily Trust a ranar Talata, ya ce ‘yan bindigar sun kira iyalan dan siyasar a ranar Lahadi.
"Sun bukaci 'yan uwansa su kai masu Naira miliyan 20 da kuma babura biyu matsayin kudin fansa."
- A cewar shugaban yankin.
Ya ce daya daga cikin ‘yan uwan dan siyasar da aka kama ya na kan tattaunawa da ‘yan fashin domin samun ragi daga kudin da suka bukata.
An sace dan siyasar a gona
Shugaban yankin ya ci gaba da cewa:
“A safiyar yau ne dan uwan wanda aka yi garkuwa da shi ya zo wurina, inda ya sanar da ni yadda ya yi magana da shugaban ‘yan bindigar.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur, bai samu damar daga wayarsa domin jin ta bakinsa kan lamarin ba.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne aka ruwaito cewa ‘yan bindigar sun yi awon gaba da dan siyasar a lokacin da ya je duba gonarsa.
'Yan bindiga sun kashe kansila
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu miyagun 'yan bindiga sun harbe wani kansila har lahira a gundumar Isu da ke karamar hukumar Onicha a jihar Ebonyi.
An rahoto cewa 'yan bindigar sun kashe kansilar mai suna Stanley Akpa Nweze tare da wani shugaban kungiyar matasan Najeriya (NYCN) reshen Onicha.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng