Tsadar Fetur: Fasinjoji a Kaduna Sun Hakura da Hawa Mota, Sun Nemawa Kansu Mafita

Tsadar Fetur: Fasinjoji a Kaduna Sun Hakura da Hawa Mota, Sun Nemawa Kansu Mafita

  • Fasinjoji da dama a Kaduna sun hakura da hawa motocin haya sakamakon tsadar da kudin biyo bayan karin kudin fetur da NNPCL ya yi
  • An ce yanzu fasinjojin sun gwammace su bi jirgin kasa da ke tashi daga Kaduna zuwa Abuja wanda farashinsa ya fi sauki kan motar haya
  • A zantawarmu da Abdullahi Rabiu Sani, ya koka kan cewa direbobi da ke tuki karkashin Bolt sun yi asara bayan karin kudin fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Yayin da farashin sufurin motoci ke kara hauhawa biyo bayan karin kudin fetur, fasinjoji da dama sun koma yin tafiye-tafiye ta jirgin kasa tsakanin Abuja da Kaduna.

Kara karanta wannan

Kungiyoyin duniya sun taso Tinubu a gaba, za a gudanar da zanga zanga a kasashe

Legit Hausa ta rahoto a yanzu gidajen man NNPC na sayar da litar fetur tsakanin N855 zuwa N897, yayin da ‘yan kasuwa ke sayar da shi tsakanin N930 zuwa N1,200.

An samu karuwar fasinjojin da ke hawa jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja
Tsadar fetur ta tilasta fasinjojin Kaduna hakura da motocin haya, sun koma hawa jirgin kasa. Hoto: @Moshoodpm
Asali: Twitter

Fetur: An kara kudin motocin haya

Rahoton jaridar Daily Trust ta nuna cewa biyo bayan karin kudin man, motocin haya da adaidaita sahu sun kara kudi da kusan kashi 40 zuwa 50.

Wani bincike ya nuna cewa an kara kudin motar haya daga Abuja zuwa Kaduna zuwa N6,000 daga N3,500.

Sabanin haka, zirga-zirgar jiragen kasa da ke tashi daga yankin Kubwa da Idu na Abuja zuwa Kaduna ya dawo zuwa N3,600 a halin yanzu.

Fasinjoji a Kaduna sun koma bin jirgin kasa

Jami’ai a tashan jirgin kasa ta Kubwa sun ce mutane yanzu na kama kujeru ana kwana daya kafin tafiyarsu sabanin yadda suka saba sayen tikiti a ranar da za su yi tafiya.

Kara karanta wannan

Zaben Kano: Masu neman takara 20 a NNPP sun fadi gwajin kwaya, NDLEA ta magantu

Wani fasinja mai suna Musa Hamza da ya je tashar daga Area 1 a Abuja a jiya, ya ce ya ji takaici saboda ya kasa samun tikitin komawa Kaduna a jirgin karfe 7 na safe.

Hamza wanda ke zaune da wani fasinja mai irin wannan matsalar, ya kara da cewa a sakamakon haka ne suka zabi bin jirgin da ya tashi daga tashar da karfe uku na rana.

Wani babban jami’in tashar da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ana kokarin bullo da karin jiragen kasa a kan hanyar saboda karuwa masu amfani da jiragen.

Abuja: Direban Bolt ya koka

A zantawarmu da Abdullahi Rabiu Sani, wani matashi da ke sana'ar tuka motar haya a tsarin Bolt a Abuja, ya koka kan cewa yanzu sana'arsu ta shiga garari.

Abdullahi Sani ya ce bayan karin kudin fetur, kamfanin Bolt bai kara kudin da ya ke cajar abokan ciniki ba, wanda hakan ke zama asara ga direbobi idan suka dauki fasinja.

Kara karanta wannan

Bayanai sun fito kan dalilin kama shugaban kwadago da DSS ta yi

"A safiyar yau na shan man N35,000, manhajar Bolt ta caji fasinjan farko da na dauka N3,500 amma ina tabbatar maka na kona man da ya fi na N5000 a tafiyar.
"Mun yi korafi na su kara waiwayar kudin da suke cajar abokan cinikinmu, sun ce za su duba, ka ga dole in hakura da aikin har sai sun duba din."

Abdullahi ya ce kamfanin Bolt na daga cikin hanyoyin da matasa a kasar nan ke samun kudaden shiga, kuma ya na da yakinin cewa za su yi abin da ya dace.

Jirgin Abuja-Kaduna ya yi hatsari

A wani labarin, mun ruwaito cewa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya murkushe wata mata mai matsakaicin shekaru a yankin Kubwa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa, hatsarin jirgin da motar da matar ke ciki ya faru ne a kasa da mintuna biyar kafin jirgin ya isa tasharsa ta Kubwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.