Rashin jirgin kasa da tsoron titi: An sayar da tikitin jirgin Azman N100,000 daga Abuja zuwa Kaduna

Rashin jirgin kasa da tsoron titi: An sayar da tikitin jirgin Azman N100,000 daga Abuja zuwa Kaduna

  • Bayan watanni biyu da yan bindiga suka kai hari tashar jirgin Kaduna, an dawo jigilar fasinjoji
  • A ranar Litnin, fasinjoji sun sayi tikitin jirgi har naira duba dari daga birnin Abuja zuwa Kaduna
  • Saboda tsoron bin titin Abuja-Kaduna, mutane sun gwammace su kashe makudan kudi don hawa jirgi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kamfanin jirgin Azman Air ya dawo jigilar fasinjoji zuwa jihar Kaduna bayan dakatad da shi tsawon watanni biyu sakamakon harin da yan bindiga suka kai tashar jirgin saman.

Jirgin Azman ya dira misalin karfe 12 na ranar Litnin, rahoton Daily Trust.

Kamfanin jirgin ya daina zuwa jihar Kaduna tun ranar 28 ga Maris bayan harin da yan bindiga masu garkuwa da mutane suka kai titin jirgin.

Rahoton ya kara da cewa a ranar Litnin, jirgin ya sauka da fasinjoji 42 inda wasu cikin fasinjojin suka biya N100,000 daga Abuja zuwa Kaduna.

Kara karanta wannan

Harin jirgin kasan Abj-Kad: An nemo 'ya'ya 8 na 'yan ta'adda, ana shirin mika musu don fansar fasinjoji

Nisan jirgin Abuja zuwa Kaduna bai wuce minti 20 ba, ama sai da fasinjoji suka biya kudin jirgi biyu; Abuja zuwa Legas da Legas zuwa Kaduna.

Jirgin da ya tashi a Abuja bai taho Kaduna kai tsaye ba sai da ya tafi Legas sannan aka taho daga Legas zuwa Kaduna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata majiya tace:

"Wannan na nuna yadda mutane ke tsoron zuwa Kaduna sakamakon rashin tsaron titin Abuja-Kaduna da dakatad da jirgin kasa."

Wani jami'in Azman ya tabbatar da labarin inda yace jirgin zai rika jigilar fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna rana daya sannan ya huta kwana daya.

Rashin jirgin kasa da tsoron titi: An sayar da tikitin jirgin Azman N100,000 daga Abuja zuwa Kaduna
Rashin jirgin kasa da tsoron titi: An sayar da tikitin jirgin Azman N100,000 daga Abuja zuwa Kaduna Hoto: Azman
Asali: UGC

Idan ba'a saki kwamandojinmu ba, ba za'a sake amfani da jirgin kasa da titin Abuja-Kaduna ba: Yan ta'adda

Yan ta'addan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna sun yi barazanar hana amfanin da titin Kaduna-Abuja gaba daya idan gwamnatin tarayya bata saki yan'uwansu ba.

Kara karanta wannan

Ka taimaka kada ta tayar damu daga gidajenmu: Mazauna garuruwan dake kan titin Abuja-Kaduna

Shugaban yan ta'addan, Abu Barrah, ya bayyana hakan ne ga Tukur Mamu, shugaban kamfanin jaridar Desert Herald.

Abu Barrah ya kara da cewa saboda su gwamnatin tarayya ta dage ranar dawo da amfani da jirgin kasan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel