"Za Mu Kai Dauki Maiduguri": Tinubu Ya Aika Sako ga Zulum bayan Ambaliyar Ruwa

"Za Mu Kai Dauki Maiduguri": Tinubu Ya Aika Sako ga Zulum bayan Ambaliyar Ruwa

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya tabbatarwa Gwamna Babagana Umara Zulum cewa gwamnatin tarayya na a shirye domin taimakawa Borno
  • Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da ambaliyar ruwa ta mamaye wasu sassan jihar Borno bayan ballewar madatsar ruwan Alau a yau
  • Shugaban kasar ya jajantawa wadanda iftila'in ya shafa, sai ya umarci hukumar ba da agajin gaggawa ta tarayya ta kai dauki Maiduguri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya bayyana matukar damuwarsa game da ambaliyar ruwa da ta mamaye wasu sassan Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Ambaliya mafi muni a cikin shekarun baya-bayan nan ta daidaita dubbunnan mazauna yankin tare da yin barna a ofishin gidan waya da asibitin koyarwa na Maiduguri.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kadu da ambaliyar ruwa a Maiduguri, ya ba Shettima sabon umarni

Shugaba Tinubu ya yi magana kan ambaliyar ruwa a Maiduguri, jihar Borno
Tinubu ya ba hukumar NEMA umarnin kai dauki ga mutanen Maiduguri bayan ambaliyar ruwa. Hoto: Audu Marte
Asali: Getty Images

Bola Tinubu ya jajantawa jihar Borno

A cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaban kasar ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata, Tinubu ya jajantawa gwamnati da al'ummar Borno.

"Shugaba Tinubu ya jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar, musamman ga iyalan da suka rasa abin dogaro da rayuwasu sakamakon ambaliyar da madatsar Alau ta haddasa.
"Yayin da hukumomin da abin ya shafa ke ci gaba da tantance irin barnar da ambaliyar ta yi, shugaban ya yi kira da a gaggauta kwashe mutanen daga yankunan da abin ya shafa."

- Bayo Onanuga.

Ambaliya: Tinubu ya ba da umarni

Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya tabbatar wa Gwamna Babagana Umara Zulum cewa gwamnatin tarayya a shirye take ta taimakawa bukatun jin kai ga mutanen da abin ya shafa.

Kara karanta wannan

An shiga fargaba, ambaliya ta wargaza maƙabarta a Maiduguri

"Ya umurci hukumar ba da agajin gaggawa ta tarayya da ta kai dauki ga wadanda ambaliyar ta shafa.
"Shugaban ya kuma jaddada kudurinsa na ba da duk wata gudunmowa da ake bukata daga gwamnatin tarayya domin tallafawa jihar a wannan mawuyacin lokaci."

- A cewar sanarwar.

Tinubu ya tura Shettima zuwa Borno

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya ba Kashim Shettima umarnin barin Abuja zuwa Maiduguri, babban birnin Borno kan ambaliyar ruwan.

Mataimakin shugaban kasar ne ya bayyana hakan a wani taro, wanda ya ce gwamnatin Tinubu na jajantawa wadanda iftila'in ambaliyar ruwa ya rutsa da su a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.