Shugaban Majalisa Ya Koka da Sace Mutane a Asibitin Kaduna, Ya Fadi Abin da Ake Bukata

Shugaban Majalisa Ya Koka da Sace Mutane a Asibitin Kaduna, Ya Fadi Abin da Ake Bukata

  • Shugaban majalisar wakilan kasar nan, Tajuddeen Abbas ya yi tir da yadda yan bindiga ke ci gaba da cin zarafin yan kasar nan son ransu
  • Shugaban ya bayyana rashin jin dadin yadda miyagun yan ta'addan su ka sace wasu ma'aikatan jinya da marasa lafiya masu yawa a Kaduna
  • Hon. Tajuddeen Abbas ya umarci jami'an tsaronl su yi duk abin da ya dace wajen ceto mutanen da aka sace tare da kawo karshen ta'addanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Shugaban majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas ya bayyana takaicin yadda yan bindiga su ka sace wasu ma'aikatan jinya a Kaduna.

Kara karanta wannan

Mazauna Kano sun tashi da takaici, an tsinci jaririya a ƙarkashin tayar mota

Haka kuma miyagun yan bindigar sun kwashe marasa lafiya da har yanzu ba a kai ga sanin adadinsu ba lokacin da su ka farmaki asibitin da ke karamar hukumar Birnin Gwari.

Majalisa
Shugaban majalisa ya koka kan ƙaruwar ta'addanci Hoto: Abbas Tajuddeen
Asali: Facebook

A sakon da shugaban majalisar ya wallafa a shafinsa na Facebook, Hon. Tajuddeen Abbas ya ce lamarin ayyukan yan bindiga ya yi yawa a kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban majalisa ya koka kan yan ta'adda

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Rt. Hon. Tajuddeen Abbas ya bayyana takaici kan karuwar ayyukan yan bindiga a fadin kasar nan. Ya bayyana takaicinsa ne bayan yan bindiga sun kutsa asibitin sha-ka-tafi da ke kauyen Layin Dan a mazabar Kuyello, karamar hukumar Birnin-Gwari a Kaduna.

"Jami'an tsaro ku tashi tsaye" - Shugaban majalisa

Hon. Tajuddeen Abbas ya ce zama bai kama jami'an tsaron kasar nan ba, dole su tashi tsaye wajen ceto jami'an lafiya da masu jinya da aka sace.

Kara karanta wannan

"Na yi wasiyya idan an sace ni," Sheikh Bello Yabo ya sha alwashin cafko yan bindiga

Ya ce yanzu haka yan bindiga na gudanar da ayyukan ta'addanci ba tare da wata fargaba ba, amma lokaci ya yi na daukar matakan gaggawa.

Kaduna: Yan ta'adda sun sace bayin Allah

A wani labarin, kun ji cewa wasu miyagun yan ta'adda sun kai farmaki wani karamin asibiti a karamar hukumar Birnin Bwari, inda su ka sace mutane da dama.

Shugaban yan banga a yankin, Musa Alhassan ya bayyana cewa sai da maharan su ka shiga wata makarantar sakandare a yankin, inda daga bisani su ka afka asibitin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.