Fitaccen Mawaki Musulmi Ya Zabgawa Malamin Addini Mari a Bidiyo, Ya Fadi Dalili
- Mawakin Najeriya, Habeeb Olalomi Badmus ya mari wani Fasto da ke wa'azi kusa da shagonsa na siyar da kayan shaye-shaye
- Mawakin da ake kira Portable ya gargadi Faston da ya bar kusa da shagonsa inda ya ke zargin yana damun abokan huldarsa
- An yada faifan bidiyon a kafofin sadarwa inda mutane da dama suka goyi bayansa yayin da wasu ke cewa abin da ya yi ya kauce hanya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagos - Fitaccen mawaki a Najeriya, Habeeb Olalomi Badmus ya mari wani Fasto saboda wa'azi a wurin kasuwancinsa.
Mawakin da aka fi sani da Portable ya mari Faston ne kan zargin zai kora masa abokan hulda a shagonsa na shaye-shaye.
Yadda mawaki ya mari Fasto saboda wa'azi
An yada bidiyon ne a shafin Instagram wanda ya dauki hankulan mutane da dama da suka tofa albarkacin bakinsu.
An gano Portable na umartan Faston ya bar kusa da shagonsa saboda yana addabar abokan huldarsa a wurin.
Daga bisani mawakin ya tunkari Faston tare da cewa yana damunsa inda ya zabga masa mari.
Portable ya fadawa Faston cewa ya yi addu'a a gida kafin ya fito domin haka babu wanda zai koya masa addu'a.
"Ka zo harkar kasuwanci ne ko ka kawo kudi?, kai mahaukaci ne? ka zo nan kana ta ihu a kai na."
"Kafin na bar gida, na yi addu'a, ku fada masa ya yi gaba, kudi ne muke tsammani a nan."
- Portable
Mawaki ya caccaki masu zanga-zanga a Najeriya
Kun ji cewa Mawaki Habeeb Okikiola ya dira kan masu zanga-zanga inda ya ce talauci da rashin aiki ne yake yaudarar matasan da ke son fita.
Mawakin da aka fi sani da Portable ya ce a baya ya fita zanga-zanga amma lokacin ba shi da ko kwabo amma yanzu ya tsira daga talauci.
Portable yayi wannan martani ne yayin da matasa a Najeriya suka shirya fita zanga-zanga a ranar 1 ga watan Agustan 2024 a kasar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng