Gwamna Zai Fara ba Mutane Bindiga a domin Gwabzawa da 'Yan Ta’addan Arewa

Gwamna Zai Fara ba Mutane Bindiga a domin Gwabzawa da 'Yan Ta’addan Arewa

  • Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya nuna takaici kan yadda yan bindiga ke kashe mutane da sace su a Arewacin Najeriya
  • Dikko Umaru Radda ya ce a shirye yake ya ba mutane bindigogi domin su rika fafatawa da yan ta'adda masu garkuwa da mutane a Katsina
  • Gwamnan ya bayyana matakan da za a dauka kafin a fara ba mutane damar mallakar bindiga domin kare kansu daga sharrin yan ta'addar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya nuna amincewa kan ba mutane damar mallakar bindiga.

Gwamna Dikko Umaru Radda ya ce hakan zai taimaka wajen kawo karshen yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

"Akwai barazana": Ribadu ya fadi hanya 1 na inganta darajar Naira

Gwamna Radda
Za a ba mutane damar mallakar bindiga a Katsina. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Asali: Facebook

Dikko Umaru Radda ya fadi haka ne a wata hira da ya yi da DW Hausa kamar yadda ta wallafa bidiyon hirar a shafinta na Facebook.

Za a ba mutane damar mallakar bindiga

Gwamna Dikko Umaru Radda ya ce a shirye yake ya samar da bindigogi ga mutane a jihar Katsina.

Dikko Radda ya bayyana cewa hakan ne kawai hanyar da mutane za su kare kansu daga wulakancin da yan bindiga ke musu.

Sharadin ba mutane bindiga a Katsina

Gwamna Dikko Radda ya ce duk waɗanda suke so a ba su bindiga dole su hada kan matasan garinsu kuma su sanar ga gwamanti.

Ya ce idan suka sanar da gwamnati za a ba su horo na musamman sai a ba su bindigogin da jami'an tsaro suka yarda a ba su domin kare kansu.

Kara karanta wannan

An samu asarar rai bayan gini ya sake rikitowa a Kano

Yan bindiga na da manyan makamai

Gwamna Dikko Radda ta ce maganar cewa yan bindiga na da makaman da suka fi na al'umma ba za ta hana jama'a mallakar bindiga ba.

Ya ce ana zuzuta lamarin ne kuma al'umma suna da yawa sosai kuma sau da yawa yan ta'addar ba sa zuwa gari da yawa sosai saboda haka za a iya fafatawa da su.

Bello Yabo ya yi magana kan yan bindiga

A wani rahoton, kun ji cewa shahararren malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Bello Yabo ya yi martani kan masu masa gargadi kan yin nasiha ga yan bindiga.

Sheikh Bello Yabo ya ce ko za a dauki ransa ba zai daina magana kan yan bindiga ba saboda hakan ne aikin da Allah ya daura nasa na wa'azi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng