'Buhari Ya na Daura Ya na Yi wa 'Yan Najeriya Dariyar Halin da Suke Ciki' Inji Kakakin Jonathan

'Buhari Ya na Daura Ya na Yi wa 'Yan Najeriya Dariyar Halin da Suke Ciki' Inji Kakakin Jonathan

  • Tsohon mai magana da yawun Goodluck Jonathan, Reuben Abati ya ce Bola Tinubu ya jefa 'yan Najeriya a mawuyacin hali
  • A cewar Abati yanzu Shugaba Muhammadu Buhari na Daura yana yiw a 'yan Najeriya dariyar halin matsin tattalin da suke ciki
  • Abati ya soki 'yan Kudu maso Yamma da ke ikirarin tattalin arziki zai gyaru a hannunsu, yana mai cewa ba a ga canjin komai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gogaggen dan jarida kuma tsohon mai magana da yawun Goodluck Jonathan, Reuben Abati ya yi magana kan matsin tattalin arziki da ake fama da shi a kasar nan.

A ranar Litinin, Dakta Reuben Abati ya ce tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya na garinsa na Daura a Katsina yana yi wa 'yan Najeriya dariya kan halin da kasar nan ke ciki.

Kara karanta wannan

"Mutane za su wahala": Atiku ya yi adawa da shirin kara hajari, ya gargadi Tinubu

Reuben Abati ya ce Buhari na Daura ya na yiwa 'yan Najeriya dariya
Matsin tattali: Abati ya hasasho abin da Buhari ke yi a Daura. Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Dakta Abati, wanda shi ne jigo a cikin shirin safe na Arise TV, ya bayyana cewa Najeriya na cikin wani mawuyacin hali karkashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

"Buhari na yi wa Najeriya dariya" - Abati

A cewarsa, magajin Buhari (Bola Tinubu) ya gaza tafiyar da harkokin tattalin arziki, duk da ikirarin gwanintarsa daga yankin Kudu maso Yamma.

"Yanzu mun tsinci kanmu cikin wani yanayi da Shugaban Muhammadu Buhari, wanda a yanzu ke zaune a kauyensa Daura da ke Katsina, zai rika kallo yana yi mana dariya.
"Zai ce, 'shi kenan. Ina tunanin wadannan Yarabawan sun ce sun san tattalin arziki. Shikenan, tattalin arzikin yanzu na hannunsu. Sun durkusar da shi kasa. Sun yi wadaka da shi."

"Tsire ya koma N1850" - Abati

Reuben Abati ya ci gaba da cewa cin fuska ne ga 'yan Kudu maso Yamma kan yadda ake tafiyar da tattalin arzikin kasar yana mai cewa ba abin da kasar ta gani na ci gaba har yanzu.

Kara karanta wannan

"Buhari ma ya fi shi": NLC ta fadi gwamnatoci 2 da suka ɗara mulkin Tinubu

A cewarsa:

“Makarantu sun kara kudin makaranta. Ko kun san tsire yanzu ya koma N1850? Litar man fetur kuwa ta koma N1200 har N1250 a wasu sassan kasar nan.
"Rayuwa ta yi tsada. Kuma wadanda suka yi ikirarin cewa za su cire mutane daga kangi, yanzu su ne ke kara jefa mutane a wahala, wanda ya kai har ana so a kara yin wata zanga zanga."

Kalli hirar a nan kasa:

"Buhari ya jawo matsin tattali" - Gabam

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban jam'iyyar adawa ta SDP, Shehu Gabam ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari ce ta jefa Najeriya a matsin tattalin da ta ke ciki a yanzu.

Duk da dai ya na ganin gwamnatin Bola Tinubu za ta iya magance matsalolin, amma Gabam ya ce dole sai an bi sannu a hankali domin kar a kuma jefa 'yan kasar a mawuyacin hali.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.