Bayan Jan Kafa daga Matatar Dangote, Yan Kasuwa Sun Nemi Hanyar Samun Fetur

Bayan Jan Kafa daga Matatar Dangote, Yan Kasuwa Sun Nemi Hanyar Samun Fetur

  • Alamu na nuna cewa akwai yiwuwar 'yan kasuwar kasar nan dake harkar man fetur su nemi hanyar samun fetur da kansu
  • Wannan na zuwa ne bayan an samu jan kafa daga matatar man fetur ta Dangote da ake sa ran za ta wadata yan kasuwar da fetur
  • A bangarensa, kamfanin NNPCL ya bayyana cewa ba shi kadai ne zai dauko mai daga matatar Dangote domin yan kasuwa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Akwai alamun masu kasuwancin man fetur a kasar nan za su fara dauko man fetur daga kasashen ketare.

Kara karanta wannan

Sharudan NNPCL ka iya kawo cikas ga matatar Dangote bayan kara kudin mai

Matakin na zuwa bayan kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya bayyana cewa zai dauko fetur daga matatar Dangote idan farashinsa ya fi na kasuwar duniya arha.

Dangote
Yan kasuwa za su shiga neman fetur Hoto: Dangote Industries
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa kalaman NNPCL na zuwa ne bayan shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya ce kamfanin mai na kasa kawai ya ke jira.

"Kowa ya dauko fetur daga Dangote," NNPCL

Kamfanin mai na kasa (NNPC) ya bayyana cewa kowane dan kasuwa zai iya dauko fetur daga matatar Dangote ba sai an jira shi ba.

Legit.ng ta wallafa cewa NNPCL ya kara da cewa matatar Dangote za ta iya sayarwa duk dan kasuwar da ke son hulda da ita fetur.

Dangote: An magantu kan samuwar fetur

The Street Journal ta wallafa cewa 'yan kasuwa sun bayyana damuwa kan rashin cimma matsaya tsakanin kamfanin NNPCL da matatar Dangote.

Kara karanta wannan

Dangote: NNPC ya ba matatun Najeriya ikon sayar da fetur kai tsaye ga 'yan kasuwa

Yan kasuwar na bayyana cewa za su tafi neman man fetur a dukkanin wuraren da su ke da yakinin za su same shi da sauki.

Dangote: NNPCL ya fadi sharadin sayen fetur

A wani labarin kun ji cewa kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya fadi sharadin da zai dauko fetur daga matatar Dangote, a lokacin da yan kasar nan ke fama da tsadar fetur.

Kamfanin NNPCL ya bayyana cewa zai rika sayen fetur daga matatar Dangote kawai idan ya fi sauki a kan yadda ake sayarwa a kasuwar duniya, kuma kalaman sun zo a lokacin da ake jiran fetur din.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.