Kashe Shanun Bello Turji Ya Jefa Mazauna Zamfara a Matsala, Za Su Biya N30m

Kashe Shanun Bello Turji Ya Jefa Mazauna Zamfara a Matsala, Za Su Biya N30m

  • Rahotanni sun bayyana cewa dan ta'addan daji, Bello Turji zai karbi diyyar Naira miliyan 30 daga mazauna kauyen Moriki da ke jihar Zamfara
  • An ce Turji ya tilasta mazauna kauyen biyan wadannan kudi ne bayan da wani kwamandan soji da aka kawo yankin ya kashe masa shanu
  • Duk da cewa kwamandan sojin ya shawarci mazauna yankin da ka da su biya kudin, an ce mutanen suna cike da tsoron ukubar Bello Turji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Mazauna kauyen Moriki da ke Zamfara sun shiga tashin hankali tun bayan da aka rahoto cewa jami'an sojojin da aka girke a kauyen sun kashe shanun Bello Turji.

An ce sabon kwamandan rundunar sojin da aka girke a kauyen Moriki ne ya kashe shanun Bello Turji, lamarin da dan ta'addan ya ce ba zai lamunta ba.

Kara karanta wannan

Bayan kara kudin mai: Gwamnati ta fadi lokacin da fetur zai wadata a fadin Najeriya

Bello Turji ya kakaba diyyar N30m ga mazauna Zamfara bayan kashe shanunsa
Zamfara: Mazauna Moriki za su biya Bello Turji diyyar N30m na kashe shanunsa. Hoto: @bulamabukarti
Asali: Twitter

Zamfara: Za a biya Turji N30m

Fitaccen dan jarida, Bulama Bukarti, ya wallafa a shafinsa na X cewa an yi ciniki tsakanin Turji da mazauna Moriki kan kudin da za su biya matsayin diyyar kashe shanunsa.

Daga Naira miliyan 50 da Bello Turji ya nema daga 'yan kauyen, Bukarti ya rahoto cewa yanzu an cimma matsaya kan mutanen su biya Naira miliyan 30.

An ce kowanne gida za su biya N10,000 yayin da duk wani baligi marar aure zai biya N2,000.

Duk da cewa kwamandan sojojin ya ba mazauna kauyen shawarar ka da su biya kudin tare da alkawarin ba zai kara taba shanun Turji ba, tsoro bai bar zukatan 'yan Moriki ba.

Mazauna Moriki na tsoron Turji

An rahoto cewa fargabar cewa wa'adin da dan ta'addan ya deba na shirin karewa, mazauna kauyen Moriki sun ci gaba da tattara abin da suke dashi domin biyan diyyar.

Kara karanta wannan

"Babu wanda ya tsira": Miyagu sun fasa ofishin gwamnan APC, sun yashe kaya

Mazauna kauyen na tsoron cewa Bello Turji zai iya saukar da ukubarsa a kansu idan har suka ki biyan kudin ba tare da wani ya cece su daga zaluncinsa ba.

A harin yanzu, an ce kimanin 'yan siyasar kauyen 15 da wasu masu fada aji ke hannun rundunar Bello Turji bayan da ya yi garkuwa da su a yankin Moriki duk da zaman sojoji a wajen.

Turji ya nunawa Matawalle yatsa

A wani labarin, mun ruwaito cewa rikakken ta'addan daji, Bello Turji ya zargi tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle da goyon bayan ayyukan ta'addanci a jihar.

A cikin wani faifan bidiyo da ya saki, Turji ya ce yana da hujjoji da zai kare zargin da ya yi na cewa gwamnatin da ta shude a Zamfara ce ta daurewa ta'addanci gindi a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.