An Birne Shi bayan Gwamnati Ta Wulakanta Dangin Mutumin da Ya Kirkiro Tutar Najeiya
- Taiwo Akinkunmi ya tafi gidan barzahu sama da shekara bayan ya rasu ya na mai shekara kusan 90 da haihuwa
- ‘Yanuwan marigayin sun hakura sun birne shi tun da sun fahimci babu ranar cika alkawarin gwamnatin tarayya
- Gwamnatin Najeriya ta dauki alkawari za ta dauki nauyin birne shi amma kusan shekara da yin hakan babu labari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Oyo - 'Yanuwan Taiwo Akinkunmi sun gaji da gafara sa ba su ga hako ba, sun birne danuwansu bayan dogon jiran wata da watanni.
Dangin Taiwo Akinkunmi sun birne shi ne bayan shekara guda kenan su na jiran gwamnatin Najeriya ta dauki dawainiyar hidimar.
An manta da wanda ya zana tutar Najeriya
Rahoton Punch ya ce ya kamata a ce gwamnatin tarayya ta dauki nauyin biki da jana’izar Akinkunmi saboda kokarin da ya yi wa kasarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marigayi wanda ya rasu ya na shekara 87 shi ne mutumin da ya kirkiro tutar Najeriya.
Yaron marigayin mai suna Akinwumi Akinkunmi ya bayyana cewa sun dade su na sauraron gwamnati ta cika alkawarin da ta dauka.
Akinwumi Akinkunmi ya shaidawa BBC a tsakiyar makon nan an shafe watanni amma ba su ga alamun za a birne mahaifinsu ba.
A cewar yaron marigayin, duk rana su na kashe N2, 000 domin ajiye shi a dakin gawa.
Gwamnatin Oyo ta sa na birne Taiwo Akinkunmi
Saboda haka ne gwamnatin jihar Oyo ta yi hobbasa domin ganin an birne tsohon kuma aka shirya biki daga ranar 4 ga watan Satumba.
An tsaida ranar Laraban zuwa Juma’a 7 ga watan Satumba domin jana’izar a Ibadan. MSN ta ce Dr. Thomas Olayode ya soki bata lokacin.
Gwamnati ta wulakanta Marigayi Taiwo Akinkunmi
Jawabin da dangin suka fitar ya bayyana cewa sun lura cibiyar wayar da kan al’adu ta tarayya aka daurawa nauyin jana’izar da farko.
Daily Post ta rahoto cewa ganin shirun ya yi yawa, dangin su ka yi watsi da gwamnati bayan an daina daukar kiran wayansu.
Mista Akinwumi ya ce sun ji tsoron jinkirin da aka yi ya bata sunan mahaifinsu wanda ya rayu a matsayin mutum mai basira da daraja.
Mace-mace da aka yi a Najeriya
Ba a wuce mako da rasuwar Sarkin Gobir ba sai aka yi ta fama da rashe-rashe a Najeriya, rahoton nan ya tattaro rashin da aka yi.
Mai martaba Hakimin Bichi, Mahaifiyar shugaba Umaru Yar’adua da Uwargidar Sarkin Zazzau Shehu Idris sun cika kwanan nan.
Asali: Legit.ng