Muhimman bayanai 5 da baku sani ba game da Mista Taiwo Akinkunmi, wanda ya kirkiro tutar Najeriya

Muhimman bayanai 5 da baku sani ba game da Mista Taiwo Akinkunmi, wanda ya kirkiro tutar Najeriya

Tabbas tarihin Najeriya baya kammaluwa ba tare da an fadi sunan dattijon arzikin nan ba da ya yi anfani da bsiyar sa ya dauki tsawon lokaci sannan ya kirkiro tutar Najeriya da yanzu haka ake anfani da ita.

Tarihi dai ya nuna cewa tutar ta Najeriya dai wani bawan Allah ne mai suna Mista Michael Taiwo Akinkunmi da ke da shekaru 23 kacal a wancan lokacin ya kirkire ta a shekarar 1958 kafin daga bisani a amince da ita sannan a kaddamar da ita a ranar 1 ga watan Oktoba shekara ta 1960.

Muhimman bayanai 5 da baku sani ba game da Mista Taiwo Akinkunmi, wanda ya kirkiro tutar Najeriya
Muhimman bayanai 5 da baku sani ba game da Mista Taiwo Akinkunmi, wanda ya kirkiro tutar Najeriya

KU KARANTA: An bukaci Buhari yayi murabus

Legit.ng kamar yadda ta saba, ta yi bincike mai zurfi sannan kuma ta zakulo maku muhimman bayanai akalla 5 da ya kamata ku sani game da hazikin dattajon:

1. Ya lashe gasar kirkirar tutar ne lokacin yana da shekaru 23 a duniya.

2. Naira 42,150 ne aka bashi a matsayin kyautar sa.

3. Yanzu haka dai Mista Taiwo Akinkunmi shekarun sa 82 a duniya.

4. Tuni yayi ritaya daga aikin gwamnati amatsayin mataimakin Darakta

5. A shekarar 2014 Gwamnatin shugaba Jonathan ta karrama shi da kyautar girmamawa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng