Najeriya @60: Tarihin mutumin da ya kirkiri tutar Najeriya da ma'anar kalolin jikinta

Najeriya @60: Tarihin mutumin da ya kirkiri tutar Najeriya da ma'anar kalolin jikinta

- A yayin da Najeriya ke bukukuwan murnar cika shekaru 60 da samun 'yanci a yau Alhamis, 1 ga watan Oktoba, Legit.ng Hausa ta sake kawo tarihin mutumin da ya kirkiri tutar Najeriya

- Har yanzu mutumin mai suna Michael Taiwo Akinkunmi yana nan a raye, kuma babu alamun cewa ya tara wata dukiya

- Hira da Aljazeera a shekarar 2018 ta bawa dattijo Akinkunmi damar fadin yadda ya yi tunanin tutar, launukan jikinta da kuma ma'anarsu

Michael Taiwo Akinkunmi shine sunan mutumin da ya lashe gasar kirkirar tutar Najeriya a lokacin da ya ke karatun injiniya a 'Norwood Technical College London' da ke kasar Ingila a shekarar 1959.

Dattijo Akinkunmi ya na da shekarun haihuwa 23 lokacin da ya shiga gasar kirkirar tutar Najeriya kuma ya samu kyautar kudi fan 100 (Dala 281) da kuma samun matsuguni cikin kundin tarihin Najeriya sakamakon nasarar da ya samu.

Yanzu haka Mista Akinkunmi ya na rayuwa ne a matsayin dan fansho a mahaifarsa, garin Ibadan, da ke jihar Oyo.

Babu wata alama da ke nuna cewa ya tara dukiya, saboda gidansa a cikin unguwar talakawa ya ke, irin unguwnnin da ko hanyar mota babu.

DUBA WANNAN: Babbar magana: Buhari ya yi amai ya lashe ranar jajiberin bikin Nigeria @60

Mista Akinkunmi ya bayyana cewa tafiya mai tsawo da ya yi tun bayan ritayarsa daga aiki, ita ce zuwa Abuja a shekarar 2014 lokacin da tsohon shugaban kasa Jonathan ya karrama shi.

A cewarsa, tsohon shugaban kasa Jonathan ya kirkirar masa albashin dundundun, wanda ya bayyana cewa duk wata ana biyansa har yanzu.

Najeriya @60: Tarihin mutumin da ya kirkiri tutar Najeriya da ma'anar kalolin jikinta
Michael Taiwo Akinkunmi @legit.ng
Asali: Twitter

Akinkunmi ya gamu da matsalar mantuwa, ba komai ya ke iya tunawa ba, domin ya bayyana cewa ba zai iya tuna mai tsohon shugaban kasa Jonathan ya fada masa ba lokacin da ya gayyace shi.

DUBA WANNAN: Ana shirin murnar Nigeria @60, gwamnatin Ogun ta sanya dokar ta baci

Kazalika ya kasa tuna sunayen abokansa na kuruciya, hasali ma, ya gaza tuna cikakken sunan makarantar da ya halarta a Ingila, sannan ya kasa tuna dalilin da yasa akayi masa tiyata jim kadan bayan ya bar aiki a shekarar 1994.

Yanzu haka Akinkunmi ya na da shekaru 82 da haihuwa kuma fentin gidansa kore da fari ne kamar yadda yayi fentin tutar Najeriya.

''Kalar tutar na nufin nomanmu, arzikinmu, mutuncinmu, da kimar mu a idon duniya,'' a cewar Akinkunmi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng