Halin da Ake Ciki a Kano Watanni 3 da Abba Ya Kawo Dokar Ta Baci a Harkar Ilmi

Halin da Ake Ciki a Kano Watanni 3 da Abba Ya Kawo Dokar Ta Baci a Harkar Ilmi

  • Abba Kabir Yusuf ya sa dokar ta-baci a bangaren ilmi saboda kawo cigaba a karatun zamani a jihar Kano
  • Gwamnan ya ce magabacinsa watau Abdullahi Umar Ganduje ya yi sakaci a shekaru takwas da ya yi a ofis
  • Gwamnatin NNPP ta ware kudi ana gyara makarantu, gina sababbin aji da kuma samar da kayan karatu a Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - A watan Yunin 2024, gwamna Abba Kabir Yusuf ya sa dokar ta-baci a kan harkar ilmi domin ya farfado da kimar harkar.

Gwamnatin NNPP ta zargi Mai girma Abdullahi Umar Ganduje da jawowa bangaren ilmi koma-baya a lokacin da ya yi mulkin Kano.

Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf a wata makaranta a Kano Hoto: Ibrahim Adam
Asali: Facebook

Tasirin dokar ta-baci da Abba ya sanya

Kara karanta wannan

Ana kuka da tsadar mai, Gwamna a Arewa ya cire tuta wurin kawowa al'umma sauki

Zuwa yanzu an fara samun cigaba a harkar ilmin zamani kamar yadda wani hadimin gwamnan na Kano ya shaida a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Salisu Yahaya Hotoro ya bayyana inda aka kwana, watanni da sa dokar ta-baci a harkar.

A sanarwar da ya fitar mai kunshe da bayanin nasarorin da aka samu da wadanda ake kai, ya ce ana ta gyaran makarantu a Kano.

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai tsaya nan ba, Malam Salisu Yahaya Hotoro ya ce ana kokarin inganta dakunan bincike har 300.

Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa gwamnatin NNPP a karkashin jagorancin Abba Yusuf ta dauki malaman makaranta na BESDA.

Nasarorin da gwamnatin Abba ta samu

1. Ana kokarin samar da rigunan makaranta da kayan karantu domin dalibai

2. Gyaran gine-ginen makarantu da kuma samar da tebura da kujeru a wasu makarantun gwamnati (Ana kan aiki, an kuma kammala wasu)

Kara karanta wannan

"Kun matsawa masu zanga zanga maimakon 'yan ta'adda," Atiku ya caccaki Tinubu

3. Yin garambuwal ga dakunan bincike (ana kan aiki)

4. Daukar malaman makarantan BESDA 5, 632 da suka cancanta (an kammala)

5. Daukar karin malamai 10, 000 (ana kan aiki)

Gwamna Abba zai inganta ilmi mai zurfi

Hadimin gwamnan ya ce wadannan cigaba ne da aka samu a makarantun firamare zuwa na gaba da su da ke karkashin gwamnati.

Nan gaba kuma za a ji hobbasa da gwamnatin Kano ta ke yi domin inganta harkar ilmi mai zurfi a manyan makarantu da jami’o’i.

Kwamishinan Ganduje ya soki gwamnatin Abba

Sanusi Sa'id Kiru ya rike kwamishina a zamanin Abdullahi Ganduje, ana da labarin yadda ya soki gyara makarantun Kano da ake yi.

Tsohon kwamishinan harkar ilmin ya ce ba da kudin da gwamnatin NNPP ta samo ake kokarin inganta ilmi ba, tallafi ne daga ketare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng