Gwamnatin Sokoto Ta Fadi Abin da Yasa Bello Turji Ya Sake Fitar da Sabon Bidiyo

Gwamnatin Sokoto Ta Fadi Abin da Yasa Bello Turji Ya Sake Fitar da Sabon Bidiyo

  • Bayan ganin sabon bidiyon dan ta'adda, Bello Turji, gwamnatin Sokoto ta yi magana kan dalilin aika-aikar
  • Gwamnatin Sokoto ta ce Turji ya rikide ne saboda ganin shirin karar da su da Gwamna Ahmed Aliyu ke yi
  • Hakan ya biyo bayan fitar da wani sabon bidiyo da Bello Turji ya yi a jiya Laraba 4 ga watan Satumbar 2024

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Gwamnatin jihar Sokoto ta yi magana kan sabon bidiyon da dan ta'adda, Bello Turji ya fitar.

Gwamnatin ta ce gaba daya Bello Turji ya rikice ne ganin yadda Gwamna Ahmed Aliyu ya shirya karar da su.

Gwamnatin Sokoto ta magantu kan sabon bidiyon Bello Turji
Bayan sabon bidiyon Bello Turji, Gwamnatin Sokoto ta ce dan ta'addan ya rikide. Hoto: @honnaseerbazzah.
Asali: Twitter

Bello Turji: Gwamnatin Sokoto ta yi magana

Kara karanta wannan

"Matawalle ya san komai": Malamin Musulunci ya yi tone tone kan yakar yan bindiga

Hadimin gwamnan a bangaren sadarwa ta zamani, Hon. Naseer Bazza shi ya fadi haka a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan Turji ya fitar da sabon bidiyo a jiya Laraba 4 ga watan Satumbar 2024 kan yakarsu da ake shirin yi.

A cikin faifan bidiyon, Turji ya koka kan yadda Hausawa ke son yakar Fulani inda ya ce babu wanda zai karar da wani a kasar.

Hon. Bazza ya ce Turji ya hango barazanar da ke tunkaro shi saboda matakan da Gwamna Aliyu ke dauka.

Bazza ya ce hakan na daga cikin dalilan Turji na fitar da bidiyon saboda ya hango karshensu ya zo.

Hon. Bazza ya fadi shirin Gwamna Aliyu

"Turji ya ga Gwamna Aliyu ya fitar da motoci bakwai kirar 'Hilux' ga jami'an tsaro da kuma wasu 20 da babura 70 ga 'yan sa-kai."

Kara karanta wannan

Malamin addini ya fadi hanyar da za a taimakawa gwamnatin Tinubu

"Ya kuma ga an ware babura 75 ga kananan hukumomin Isa da Sabon Birni da Gwadabawa da Goronyo da Gada da Tureta da Illela da Wurno da Rabah domin yakar yan bindiga."
"Sannan ya ga gwamnan ya ba jami'an tsaro tankokin yaki da karin alawus da kuma samar da yan sa-kai 1,000 da mambobin SSCGC 700 da JTF 350 da karin sojoji 4,000 a yankin Sokoto ta Gabas."

- Hon. Naseer Bazza

Bello Turji ya kwace motocin sojoji

Kun ji cewa an gano dan ta'adda Bello Turji da yaransa suna shewa bayan samun iko da motocin sulken sojoji guda biyu a daji.

Yan ta'addan daga bisani sun kwashe makaman da ke cikin motocin tare da banka musu wuta a jihar Zamfara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.