Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Rigamu Gidan Gaskiya, Tambuwal Ya Yi Ta'aziyya
- Aminu Waziri Tambuwal ya mika sakon ta'aziyyar rasuwar tsohon shugaban jam'iyyar PDP na jihar Sokoto, Alhaji Ibrahim Milgoma
- Tsohon gwamnan Sokoto ya ce marigayi Ibrahim Milgoma ya kasance mutumin da ya sadaukar da rayuwarsa ga hidimtawa jama'a
- An rahoto cewa tsohon shugaban jam'iyyar na PDP ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin tarayya Abuja bayan ya sha fama da rashin lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Allah ya yi wa Alhaji Ibrahim Milgoma, tsohon shugaban PDP na jihar Sokoto rasuwa a ranar Talata, 3 ga watan Satumbar 2024.
An ruwaito cewa marigayi Alhaji Ibrahim Milgoma ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Abuja bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Tsohon shugaban jam'iyyar PDP ya rasu
Mun samu labarin rasuwar tsohon shugaban PDP din ne a shafin X na tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Tambuwal ya bayyana kaduwarsa a kan mutuwar Alhaji Milgoma wanda ya bayyana shi a matsayin jajirtacce, mutumin kirki da amana.
Tsohon gwamnan ya ce:
"Cikin kaduwa na samu labarin rasuwar Alhaji Ibrahim Milgoma, tsohon shugaban PDP na Sokoto kuma tsohon shugaban hukumar babbar kasuwar Sokoto a lokacin da na ke gwamna.
"An ce ya rasu ne a daren jiya a wani asibiti da ke Abuja bayan fama da rashin lafiya."
Tambuwal ya yabi tsohon shugaban PDP
Sanata Tambuwal ya ce ya samu damar yin mu'amala da marigayin kuma zai iya bayar da shaidar cewa Alhaji Milgoma ya kasance:
"Mutum mai halaye na sadaukarwa, jajurcewa, gaskiya, da taimakon jama'a. Ya kasance ma’aikaci mai kishi wanda ya jajirce wajen yi wa al’ummar jihar Sokoto hidima."
Tsohon gwamnan na Sokoto ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan marigayi Alhaji Ibrahim Milgoma da kuma daukacin 'yan jam'iyyar PDP.
Ya kuma yi addu'ar Allah (SWT) ya jikan marigayin.
Mahaifiyar Yar'adua ta rasu
A wani labarin, mun ruwaito cewa Allah ya yiwa Hajiya Dada rasuwa. Ita ce mahaifiyar shugaba Umaru Musa Yar'Adua.
An ce Hajiya Dada ta rasu ne bayan fama da rashin lafiya a ranar Litinin, 2 ga watan Satumba, 2024, tana da shekaru 102 a duniya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng