Barazanar tayar da rikici: An bawa 'yan sanda sa'o'i 24 su damke shugaban PDP na Sokoto

Barazanar tayar da rikici: An bawa 'yan sanda sa'o'i 24 su damke shugaban PDP na Sokoto

Wasu matasa a jihar Sokoto sunyi kira ga rundunar 'yan sanda tayi gaggawan kama shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na jihar saboda barazanar tayar da rikici da ya yi gabanin zaben gwamna a jihar.

An yi ikirarin cewa shugaban na PDP ya umurci magoya bayan jam'iyyar su kashe duk wani famanen sakatare ko shugaban ma'aikatan gwamnati da jihar da ya yi kokarin sauya sakamakon zabe domin fifita jam'iyyar adawa ta APC a jihar.

A yayin da suke jawabi a taron manema labarai a ranar Talata, matasan karkashin kungiyar 'Concerned Sokoto State Youths' sun yiwa kalamar da aka ce shugaban PDP ya yi a matsayin barazana ga zaman lafiya a jihar da yunkurin tayar da yaki tsakanin 'yan siyasa marasa hakuri.

DUBA WANNAN: Cin amana: An kama wani sufeton 'yan sanda na taimakawa 'yan daba yin basaja

Barazanar tayar da rikici: Matasa sun bawa 'yan sanda sa'o'i 24 su damke shugaban PDP na Sokoto
Barazanar tayar da rikici: Matasa sun bawa 'yan sanda sa'o'i 24 su damke shugaban PDP na Sokoto
Asali: UGC

"Muna son mu janyo hankalin kowa cewa ana amfani da shugaban PDP na jihar mu domin tayar da zaune tsaye da ka iya janyo rikici da zubar da jini a sassan jihar idan har hukumomin tsaro ba su dauki mataki cikin gaggawa ba," a cewar shugaban kungiyar, Mustapha Ibrahim.

"A dalilin kalaman tayar da zaune tsaye da Alhaji Ibrahim Milgoma ya furta be muke bukatar rundunar 'yan sandan jihar da bayar da umurnin kama shugaban na PDP cikin sa'o'i 24 tare da gabatar da shi gaban kotu," inji shi.

Ibrahim ya yi kira da al'ummar jihar su fito kwansu da kwarkwata su kada kuri'arsu a ranar Asabar ba tare da wata fargaba ba.

Sai dai a martanin da jam'iyyar PDP ta musanta cewa shugabanta yana yunkurin tayar da rikici inda ta ce kawai ya yi kira ne ga magoya bayan jam'iyyar su sanya idanu a kan dabarin APC na aikata magudin zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel