Yanzu Yanzu: EFCC ta shirya gurfanar da Shagari da sauran jiga-jigan PDP a Sokoto

Yanzu Yanzu: EFCC ta shirya gurfanar da Shagari da sauran jiga-jigan PDP a Sokoto

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta shirya gurfanar da wani tsohon ministan albarkatun ruwa kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Sokoto Alhaji Murkhtar Shagari a gaban wata babban kotun tarayya dake Sokoto a ranar Talata.

Wanda za’a gurfanar tare da Shagari akwai dan takarar gwamna na PDP a zaben 2015, Sanata Abdullahi Wali, ciyaman na PDP na jihar, Alhaji Ibrahim Milgoma, wani tsohon kwamishina, Alhaji Ibrahim Gidado da kuma Alhaji Nasiru Bafarawa, kanin tsohon gwamnan jihar Attahiru Bafarawa.

Ana zargin Jiga-jigan na PDP da hada kai wajen karban makudan kudade har N500,000,000 daga Abdulrahman Ibrahim ba tare da bin ka’ida ba kafin zaben 2015.

An bayyana cewa kudin na daga cikin rabo da suka yi na dala miliyan 115 daga wani tsohon ministan man fetur domin juya sakamakon zaben.

Yanzu Yanzu: EFCC ta shirya gurfanar da Shagari da sauran jiga-jigan PDP a Sokoto
Yanzu Yanzu: EFCC ta shirya gurfanar da Shagari da sauran jiga-jigan PDP a Sokoto

Jami’an hukumar na EFCC sun kawo jiga-jigan na PDP harabar kotu da misalign karfe 8:30 na safiyar Talata, sannan kuma a yanzu haka suna jira a fara shari’a.

KU KARANTA KUMA: 2019: Ka shirya shan kashi – PDP ga Buhari

A baya Legit.ng ta ruwaito cewa brahim Shekarau da Aminu Wali da kuma Mansur Ahmed zasu bayyana a ofishin na EFCC ne akan kudaden da ake zargin sun kasa N950m, a gidan Ibrahim Shekarau gabanin zuwan zaben shekarar 2015 a tsakanin ‘yan jam’iyyarsu ta PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng