"Za Mu Bi Maku Hakkinku," Tinubu Ya Sha Alwashi kan Kisan Bayin Allah a Yobe

"Za Mu Bi Maku Hakkinku," Tinubu Ya Sha Alwashi kan Kisan Bayin Allah a Yobe

  • Gwamnatin tarayya ta sha alwashin tabbatar da adalci kan miyagun yan kungiyar ISWAP da su ka kashe mazauna Yobe
  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya dauki alkawarin biyo bayan kisan manoma akalla 87 a Mafa da ke Tarmuwa
  • Ya mika ta'azziyyarsa ga iyalan wadanda aka kashe, tare da daukar alkawarin hukunta miyagun da su ka yi danyen aikin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana takaicin harin yan kungiyar ISWAP da ya salwantar da rayukan mazauna Mafa, a karamar Tarmuwa a jihar Yobe.

A ranar Lahadi ne miyagun su ka kai mummunan hari da aka kwana biyu ba a kai irinsa kan mazauna jihar Yobe ba.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya fadi hanyar da za a taimakawa gwamnatin Tinubu

Tinubu
Bola Tinubu ya yi alkawarin za a hukunta mayakan ISWAP Hoto: Ajuri Ngelale
Asali: Facebook

A sakon da hadimin Bola Tinubu, Ajuri Ngelale ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce shugaban kasar ya yi matukar bakin cikin mummunan harin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kasar ya kuma mika ta'azziyya ga iyalan wadanda aka kashe d sauran mutanen Yobe kan mummunan harin.

Yobe: Gwamnati za ta hukunta yan ISWAP

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin tabbatar da an hukunta miyagun 'yan kungiyar ISWAP da su kashe mutane 87 a Yobe.

Bola Tinubu ya bayyana harin a matsayin aikin matsorata inda su ka kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, AIT Television ta wallafa.

Tinubu ya yi addu'a kan harin Yobe

Gwamnatin tarayya ta yi addu'ar samun sauki ga sauran mazauna Mafa a jihar Yobe da miyagu su ka kai wa hari.

Kara karanta wannan

Atiku da Obi sun yi martani kan inyamura mai ikirarin kashe yan Najeriya a Canada

Shugaban kasa Tinubu ne ya yi addu'ar, inda ya jajanta masu bisa iftila'in harin, tare da alkawarin daukar hukunci.

ISWAP ta dauki alhakin harin Yobe

A baya mun ruwaito cewa kungiyar yan ta'addan ISWAP ta ce ita ce ta kai hari garin Mafa a karamar hukumar Tarmuwa da ke jihar Yobe a ranar Lahadi.

A wasikar bayan harin da ISWAP ta fitar, ta zargi mazauna Mafa da hada kai da sojoji wajen samar masu da hanyar kashe 'ya'yan kungiyar da ke yankin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.