Awanni da Sanarwar NNPC: Zanga Zanga Ta Barke a Kan da Litar Fetur Ta Kai N1200
- Zanga zangar adawa da karin kudin mai ta barke a jihar Kano awanni bayan da kamfanin man fetur na Najeriya ya sanar da karin kudin
- An rahoto cewa daruruwan masu sana’ar adaidaita sahu suka mamaye titunan Kano domin nuna fushinsu kan karin kudin da aka yi
- Mazauna Kano da suka safa zirga-zirga a kan adaidaita sahu sun koka da illar tsadar man, inda a yanzu tafiyar N200 ta koma N350
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano — Daruruwan masu sana’ar adaidaita sahu suka mamaye titunan Kano domin gudanar da zanga-zangar nuna adawa da karin kudin fetur.
Wannan na zuwa ne yayin da farashin man fetur (PMS) ya kai N1,200 a wasu gidajen man jihar bayan da NNPCL ya canza farashin litar man fetur.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa gidajen man kamfanin NNPCL na sayar da litar fetur a kan N904 a jihar Kano a ranar Talata.
Fetur: Zanga zanga ta barke a Kano
An rahoto cewa 'yan adaidaita sahun sun mamaye gadar Dangi da ke Kano inda suka jawo cunkuson ababen hawa na tsawon awanni a yayin zanga-zangar.
Wani dan adaidaita sahu mai suna Abdulazeez Ibrahim ya ce:
"Zan iya tuna lokacin da nake sayen fetur kan N95. Muna a cikin gidan mai aka sanar da cewa an rage fetur zuwa N65, haka aka sauya farashin nan take.
"Amma yanzu komai ya tabarbare, duk abin da ya kara kudi to ba zai kara saukowa kasa ba. Shin ina ake so talaka ya saka kansa ne a Najeriya?"
Kudin adaidaita sahu ya karu
Farashin kudin adaidaita sahu yanzu ya karu, inda mutane ke korafin tsadar kudin zirga zirga a Kano.
An zantawar Legit Hausa da wata Fatima Ibrahim Daurawa ta ce a da ta saba hawa adaidaita sahu daga Gyadi Gyadi zuwa Hotoro a kan N150 zuwa N200.
Sai dai awanni da sanar da karin kudin man, Fatima Daurawa ta ce a ranar sai da aka cajeta N350, lamarin da ta ce zai jefa karatunta a garari saboda tsadar kudin abun hawa.
Fatima ta yi kira ga gwamnatin tarayyar da ta samar da na ta adaidaita sahun ko motocin haya da al'umma za su rika hawa a farashi mai sauki.
NLC ta fusata da kara kudin fetur
A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar kwadagon Najeriya (NLC) ta nuna fushinta kan karin kudin mai da kamfanin NNPCL ya yi inda ta ce gwamnatin tarayya ta yaudareta.
Kungiyar NLC ta yi ikirarin cewa kafin ta amince da tayin gwamnati na biyan N70,000 matsayin sabon mafi karancin albashi sai da aka yi mata alkawarin ba za a kara kudin mai ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng