ISWAP Ta Dauki Alhakin Kashe Mutane 87 a Yobe, Ta Bayyana Dalili
- Kungiyar ‘yan ta’addar ISWAP sun saki wata wasika da ta bayyana su a matsayin wadanda suka kai harin da ya yi ajalin mutane 87 a Yobe
- A cikin wasikar, ISWAP ta ceta kai harin ne bisa zargin mazauna yankin sun hada kai da sojoji an je an kashe 'yan kungiyarta a kwanan baya
- An ruwaito cewa ‘yan ta’adda sun kai hari garin Mafa a ranar Lahadi, inda suka kashe mutane tare da kona gidaje da shagunan da yawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Yobe - Kungiyar ‘yan ta’addar Daesh a yammacin Afirka (ISWAP) ta dauki alhakin harin da ya kai ga kashe kimanin mutane 87 a jihar Yobe.
Legit Hausa ta ruwaito yadda ‘yan ta’adda suka kai hari garin Mafa da misalin karfe 4 na yammacin ranar Lahadi, inda suka kashe mutane tare da kona gidaje da shaguna.
A cikin wata wasika da aka rubuta cikin harshen larabci kuma mayakan suka fitar, kungiyar ISWAP ta dauki alhakin kai harin, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar ISWAP ta aiko da wasika
ISWAP a cikin wasikar, ta ce ta kai wa kauyen hari ne bisa zargin bayar da bayanai ga sojoji, lamarin da ya kai ga kashe 'yan kungiyarta.
"Wannan sako ne daga sojojin daular Khalifanci a yammacin Afirka zuwa ga shugabanni, mukhtars, da sauran mazauna garin Mafa da kuma kauyukan da ke kewaye.
"Da farko mun barku kun zauna a kasarku cikin aminci. Sojojin Khalifanci ba su farmake ku ba, ko karbar kudinku, kuma ba su hana ku yin noma da kasuwanci ba.
"Har sai da jiji da kanku ya debe ku kuka fara ganin cewa yanzu wuyanku ya yi kaurin da za ku iya yiwa 'yan uwanku makarkashiya kuma ku zauna lafiya."
- A cewar wasikar.
"Dalilin kai hari Mafa" - ISWAP
Kungiyar ISWAP ta ci gaba da cewa:
“Kun cutar da ’yan’uwanmu a garin (Bangaro) da kewaye, kuma kun ba da hadin kai ga ’yan ridda wajen kashe ’yan uwanmu, kuma da muka isa yankin, ba mu cutar da ku ba.
“A maimakon haka, mun takaita ne ga wadanda hannayensu ke da jinin ’yan’uwanmu, wadanda makamansu suka kai musu hari, kamar yadda bayanin da muka samu ya nuna.
"Mun yi tunanin cewa wannan martanin da muka yi zai zama gargaɗi a gare ku cikin harshen yaƙi, kuma da tunanin za ku shiga taitayinku."
Kungiyar ISWAP ta ce gargadin da ta yi wa mazauna yankin Mafa bai shiga kunnensu ba, illa ma kara masu jiji da kai tare da sake maimaita kuskure, lamarin da ya jawo sake kai harin.
ISWAP: An kashe 'yan sa kai
A wani labarin, mun ruwaito cewa mayakan ISWAP sun kai wani mummunan farmaki a wani sansanin 'yan sa kai da ke kauyen Katarko, kusa da Gujba a jihar Yobe.
Wata majiya ta bayyana cewa 'yan sakan sun yi artabu da 'yan ta’addan na tsawon mintuna 15 inda aka kashe 'yan sa kai biyu kafin daga bisani su samu goyon bayan dakarun soji.
Asali: Legit.ng