Gwamnatin Tinubu Ta Yi Magana kan 'Umarnin' Kara Farashin Litar Man Fetur

Gwamnatin Tinubu Ta Yi Magana kan 'Umarnin' Kara Farashin Litar Man Fetur

  • Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta barranta kanta daga rahoton da ke cewa ta ba kamfanin NNPCL umarnin sayar da fetur kan sabon farashi
  • An samu bullar labarin cewa Ministan albarkatun man fetur, Heineken Lokpobiri ya umarci NNPCL ya sayar da fetur kan sama da N1000
  • Amma a martaninta, ma'aikatar fetur ta bayyana cewa ba ta da hurumin yin katsalandan a cikin yadda NNPCL ke gudanar da harkokinsa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta musanta cewa ita ce ta umarci kamfanin mai na kasa (NNPCL) da ya kara kudin man fetur zuwa N1000 zuwa sama.

Kara karanta wannan

Ana murna matatar Dangote ta fara samar da fetur, NNPCL ya kara farashin litar mai

Gwamnatin ta ce rahoton da ke yawo na cewa ministan albarkatun fetur, Heineken Lokpobiri ne ya umarci kara farashin fetur ba gaskiya ba ne.

Tinubu
Gwamnati ta musanta bayar da umarnin karin fetur Hoto: @PBATMediaCentre
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa wannan na kunshe a sanarwar da mai ba ministan albarkatun fetur shawara ta musamman, Nnemaka Okafor ta fitar a yau Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce an bullo da labarin ne domin kawo rudani a sashen man fetur na kasar nan da kawo rashin jituwa tsakanin al'umma.

"Gwamnati ba ta katsalandan a NNPCL," Minista

Jaridar The Sun ta wallafa cewa ofishin Ministan albarkatun fetur ya ce gwamnati ba ta tsoma baki kan yadda kamfanin NNPCL ke kara farashin fetur ba.

A sanarwar da mai ba ministan fetur shawara ta musamman, Nneka Okafor ta fitar, ta ce an yiwa jawabin Minista Heineken Lokpobiri gurguwar fahimta.

Kara karanta wannan

"Ku kwana da shiri," 'Yan kasuwa sun yi barazanar karuwar farashin litar fetur

Me ministan fetur ya ce kan NNPCL?

Ma'aikatar albarkatun fetur ta kasa ta ce kalaman minista Heineken Lokpobiri kan farashin fetur ba ya nufin karin farashi.

Ma'aikatar ta ce ministan na bayani ne kawai kan dalilin da ya sa ba za a iya kawo karshen safarar fetur ta barauniyar hanya zuwa kasashen waje ba.

An fara neman tsige shugaban NNPCL

A wani labarin, mazauna babban birnin tarayya Abuja sun shiga zanga-zanga a kan karancin fetur da tsadarsa, inda su ka fara neman a tsige shugaban NNPCL, Mele Kyari.

Jama'a sun fusata tare da tsunduma zanga zangar ne bayan kamfanin ya bayyana cewa tarin bashin da ake binsa zai yi barazana ga wadatar man fetur a kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.