Ana Murna Matatar Dangote Ta Fara Samar da Fetur, an Kafa Sharuda ga 'Yan Kasuwa

Ana Murna Matatar Dangote Ta Fara Samar da Fetur, an Kafa Sharuda ga 'Yan Kasuwa

  • Matatar man Aliko Danoge ta bayyana shirinta na fara samar da man fetur a Najeriya domin saukakawa al'umma
  • Matatar ta ce ta fuskanci kalubale daga 'yan kasuwa inda ta ce idan suka ki siyan kayan nata, za ta fara fitar da su ketare
  • Hakan ya biyo bayan shirya samar da fetur wanda a baya ake zargin shirin na neman samun matsala saboda 'yan kasuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Matatar man Aliko Dangote ta bayyana tsarin yadda za ta siyar da fetur ga 'yan kasuwa.

Matatar ta tabbatar da cewa za ta fitar man kasashen ketare idan har 'yan kasuwa suka ki siyan man.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun shiga uku: Gwamnati ta ba hafsoshin tsaro umarnin tarewa a Sokoto

Matatar Dangote ta koka kan halin yan kasuwa a Najeriya
Matatar man Aliko Dangote za ta fara samar da fetur a Najeriya. Hoto: Bloomberg/Contributor.
Asali: UGC

Matatar Dangote ta fara samar da fetur

Mataimakin shugaban bangaren man da kuma gas, Devakumar Edwin shi ya bayyana haka a jiya Litinin 2 ga watan Satumbar 2024, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Edwin ya ce suna fitar da man jiragen sama da kalanzir amma a wannan Lahadi 1 ga watan Satumbar 2024 an fara samar da fetur.

Ya ce babban abin farin ciki ne matatar ta fara samar da man fetur wanda zai taimaka matuka gaya, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Matatar Dangote: Yaushe aka fara fitar da fetur?

"Mu na fitar da man jiragen sama kasashen ketare da kalanzir da kuma man dizal, amma jiya mun fara samar da man fetur."
"Abin farin ciki ga kasar shi ne a yanzu mun fara samar da man fetur daga matatarmu tun ranar Lahadi 1 ga watan Satumbar 2024."

Kara karanta wannan

Zamfara: Gwamna ya ba da tallafin kudi da filaye ga wadanda ambaliya ta shafa

"Ana samun tasgaro daga daukar kayan daga Najeriya, 'yan kasuwa suna kokarin kawo cikas, muna fitar da sauran kaya, kamar fetur za mu samar da shi da yawa a kasar."
"Amma idan 'yan kasuwa suka ki siyan kayanmu, dole ne mu fitar da shi waje kamar yadda muke yi a bangaren man jiragen sama da dizal."

- Devakumar Edwin

Dangote zai fara samar da fetur

A wani labarin mai kama da wannan, kun ji cewa matatar man Dangote wacce ke a jihar Legas za ta fara siyar da man fetur a kasuwa.

Hakan na zuwa ne zuwa ne ƴan kwanaki kaɗan bayan matatar wacce za ta samar da ganguna 650,000 a kullum ta fara yin gwaje-gwaje kan fitar da man.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.