Tinubu Zai Shiga Matsala: An Gano Shirin Atiku, Obi, Kwankwaso na Hade Kansu a 2027

Tinubu Zai Shiga Matsala: An Gano Shirin Atiku, Obi, Kwankwaso na Hade Kansu a 2027

  • Shugabannin jam’iyyar PDP sun yi karin haske a kan tattaunawar da ake yi tsakanin Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso
  • PDP ta bayyana cewa ana ci gaba da tattaunawa kan yiwuwar manyan 'yan siyasar uku su hade kansu domin tunkarar babban zaben 2027
  • Mataimakin kakakin PDP na kasa, Ibrahim Abdullahi, ya fadi hakan a ranar Litinin, ya kuma yi magana kan shirin korar Tinubu da APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Jam'iyyar PDP ta ce manyan 'yan adawa uku a Najeriya na tattaunawa kan yiwuwar hade kansu gabanin babban zaben 2027.

An ce Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso suna kan tattaunawa domin cimma matsayar hadewarsu domin ceto Najeriya daga halin da take ciki.

Kara karanta wannan

"Wike ba zai zama mana kadangaren bakin tulu ba," PDP ta fadi dalilin kafa kwamitin ladabtarwa

PDP ta fadi sunayen wadanda Atiku ke kokarin hade kai da su gabanin zaben 2027
PDP tayi magana a kan kawancen Atiku, Peter Obi da Kwankwaso. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Mr. Peter Obi, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Atiku, Kwankwaso, Obi na shirin 2027

Mataimakin kakakin jam'iyyar PDP na kasa Ibrahim Abdullahi ya bayyana haka a shirin Sunrise Daily na Channels Television a ranar Litinin, 2 ga watan Satumba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Ibrahim Abdullahi, ‘yan takarar jam’iyyun adawa uku a zaben da ya gabata; PDP, NNPP da kuma LP za su ajiye bambancinsu a gefe domin korar jam'iyyar APC a zaben mai zuwa.

Ibrahim Abdullahi ya ce da a ce shugabannin jam'iyyar na baya sun magance rikicin cikin gida, da yanzu tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike, Kwankwaso da Obi suna cikin PDP.

PDP ta magantu kan zaben 2023

Ya ce idan kuwa wadannan jiga jigan siyasar suka hade waje daya, to da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da APC ba su samu nasara a zaben da ya gabata ba.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta yi magana kan zargin shirin korar Ganduje daga mukaminsa

A cewarsa:

“Mun rasa Kwankwaso, mun rasa Peter Obi, duk wadannan mutanen, ka auna abin da zai faru da suna jam’iyyarmu, za mu ci zabe ne ba ko tababa.
“APC ta ce sun samu nasarar da tazarar kuri'u miliyan daya, to ka ga da daya daga cikin wadannan da na ambata zai iya cike gibin kuri'un."

Da aka tambaye shi ko PDP na kokarin jawo Peter Obi, Kwankwaso, Wike da sauransu cikin jam’iyyar, Abdullahi ya ce:

"Tabbas, suna kan tattaunawa. Za ka ga Obi na magana da Atiku, yana magana da Nasir El-Rufai."

"Atiku zai iya kada Tinubu" - Kalu

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kungiyar GIGG, Dakta Emeka Kalu ya ce Atiku Abubakar ne kadai dan siyasar da zai iya kwace mulki daga hannun APC a 2027.

Dakta Emeka Kalu ya ce a halin da ake ciki, Najeriya na bukatar mutum kamar Atiku matsayin shugaba domin gyara tattalin arziki, magance matsalar tsaro da sauransu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.