N500 a Wata: Kungiyar Yan Fansho Ta Fusata da Adadin da Ake Biyan Wasunsu
- Kungiyar yan fansho ta kasa ta koka kan yadda ake biyan wasu daga cikin ma'aikatan da suka kammala aiki
- Kungiyar reshen jihar Kaduna ta bayyana cewa har yanzu ana biyan wasu daga cikin yan fansho N500 a wata
- Lamarin ya fi muni a jihohin da ke da arzikin man fetur duk da tarin kudin da su ke samu daga gwamnatin tarayya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Kungiyar yan fansho ta kasa (NUP) ta bayyana takaicin yadda wasu gwamnonin jihohi ke biyan ma'aikatan fansho.
Kungiyar reshen jihar Kaduna ce ta bayyana haka, inda ta ce a wasu jihohin akwai tsofaffin ma'aikatan da ake biya N500 kacal.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa sakataren kungiyar na Kaduna, Alhassan Musa ya bayyana takaici matuka kan yadda ake biyan yan fanshon.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce bai dace a rika barin rayuwar ma'aikatan da suka hidimtawa kasa a cikin wahala ta hanyar biyansu kalilan din kudi ba.
Ana wulakanta ƴan fansho
Wasu daga cikin yan fansho a jihohin da ke Kudancin kasar nan musamman jihohi masu albarkatun man fetur sun fi kowa rashin samun fansho mai kyau, cewar rahoton The Guardian.
Kungiyar yan fansho ta kasa ce ta bayyana takaicin haka, inda ta ce bai dace a ce jihohin da ke samun arzikin mai na biyan mafi karancin kudin fansho ba.
Gwamnati na biyan fanshon N3500
Sakataren kungiyar yan fansho na jihohin Arewacin kasar nan 19, Alhassan Musa ya bayyana cewa ana biyan wasu yan fansho ₦3500.
Ya ce wuraren da lamarin ke da dama dama su ne babban birnin tarayya Abuja da wasu jihohin Arewa inda ake iya biyan har N18,000 duk wata.
Gwamnati ta ware kudin biyan yan fansho
A wani labarin kun ji cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ware Naira Biliyan 6 domin biyan bashin kudin fanshon da tsofaffin ma'aikata ke bin gwamnatin Kano.
Gwamnan ya kuma bayyana matukar takaici kan tarin bashin da gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bari da ya kai Naira Biliyan 40.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng