"Abin da Na Ke Gargadi: Sheikh Gumi Ya Magantu da Bello Turji Ya Kona Motar Sojoji

"Abin da Na Ke Gargadi: Sheikh Gumi Ya Magantu da Bello Turji Ya Kona Motar Sojoji

  • Sheikh Ahmed Gumi ya magantu bayan an gano Bello Turji da tawagarsa suna kona motocin sojoji a jihar Zamfara
  • Malamin ya ce tun farko ya yi gargadi kan yadda ya kamata a shawo kan matsalar kafin ta girma haka amma babu wanda ya saurare shi
  • Sheikh Gumi ya ce a yanzu yakin ya rikide inda mayakan suke ganin kamar aikin Allah suke wanda zai yi wahalar dakilewa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Malamin Musulunci, Sheikh Ahmed Gumi ya yi magana kan yadda rashin tsaro ya yi katutu.

Malamin ya koka ne bayan yada bidiyon tawagar Bello Turji na kona motocin sojoji a jihar Zamfara.

Sheikh ya magantu bayan ganin Bello Turji yana kona motocin sojoji
Sheikh Gumi ya nuna damuwa kan yadda yan bindiga suka kara karfi a Arewa. Hoto: Dr. Ahmed Mahmud Gumi.
Asali: Facebook

Bello Turji: Sheikh ya tuno gargadinsa

Kara karanta wannan

An gano bidiyon Bello Turji yana shan alwashi bayan kwace motocin sulken sojoji

Sheikh Gumi ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook a yau Asabar 31 ga watan Agustan 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shehin malamin ya ce tun tuni ya ke gargadi kan illar barin yan ta'addan wanda ka iya sake gurbata musu tunani.

Ya ce matsalar ta fara sauya salo inda a yanzu miyagun ke ganin kaman aikin Allah suke yi a tunaninsu.

Gumi ya fadi illar 'yan ta'adda a yanzu

"Tun farko, yan bindigar na fada ne kamar na kabilanci da za a iya shawo kan matsalar da sauki."
"Na yi ta gargadi kan yadda ya kamata a shawo kan matsalar kan cewa za su iya sauya salon yakinsu amma ba a sauraren ba."
"Bambancin fadansu na baya da irin wannan shi ne ba za a iya shawo kansu ba, kamar yadda Boko Haram suka yi, suna barna amma a yanzu tunaninsu shi ne aikin Allah suke yi."

Kara karanta wannan

"Sai an dage": Sule Lamido ya yi magana kan yiwuwar kifar da Tinubu a 2027

- Sheikh Ahmed Gumi

Zamfara: Bello Turji ya kwace motocin sojoji

Kun ji cewa an yi ta yada wani faifan bidiyo mai tayar da hankali da 'yan ta'adda ke bankawa motocin sulke na sojoji wuta.

An ruwaito cewa lamarin ya faru ne a karamar hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne bayan sojoji sun janye daga kai harin da suka yi niyya saboda wasu matsaloli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.