Jerin Duka Shugabannin Hukumar DSS 10 da Aka Yi daga Shekarar 1986 zuwa 2024
Abuja - Ana da labarin yadda aka haifi hukumar DSS ko kuwa SSS lokacin Janar Ibrahim Badamasi Babangida yana mulkin soja.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
A makon da ya gabata aka ji shugaban kasa mai-ci Bola Tinubu ya nada Adeola Ajayi ya canji Yusuf Bichi a matsayin shugaban DSS.
Bayanan da aka samu daga shafin hukumar DSS sun nuna Adeola Ajayi ya shiga ofis.
A wannan karo, Legit Hausa ta kawo maku sunayen shugabannin da hukumar tayi a tarihin kusan shekaru 40 da kafuwarta a kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sunayen shugabannin hukumar DSS
1. Ismail Gwarzo
A lokacin da Ibrahim Babangida ya kafa DSS a 1986, Ismail Gwarzo daga jihar Kano ya fara rike ta, ya bar ofis ne a Satumban 1990.
2. Albert Horsfall
Albert Horsfall wanda da suka aka kafa NSO shi ne ya shugabanci hukumar DSS daga 1990 zuwa 1992, asalinsa jami’in ‘dan sanda ne.
3. Peter Nwaoduah
Shugaba na uku da aka yi shi ne Cif Peter Nwaoduah, ya rike hukumar tsakanin 1992 da 1998 - lokacin da Janar Sani Abacha ya rasu.
4. Kayode Are
Olusegun Obasanjo ya dauko tsohon Kanal na soja, Lateef Kayode Are ya zama shugaban DSS a lokacinsa, daga baya ya zama NSA.
5. Afakariya Gadzama
Lokacin da Ummaru Yar’adua ya zama shugaban kasa sai ya kawo Afakariya Gadzama, ya jagoranci DSS ne daga 2007 zuwa 2010.
6. Ita Ekpeyong
Daga 2010 zuwa 2015 da Mai girma Goodluck Jonathan ya mulki Najeriya, Ita Esien Ekpeyong ne shugaban jami’an tsaron na fararen kaya.
7. Lawal Musa Daura
A Yulin 2015 Muhammadu Buhari ya dawo da Lawal Daura DSS, ya rike Darekta Janar na hukumar zuwa lokacin da aka tsige shi a Agustan 2018.
8. Mathew Seiyefa
Shugaban rikon da Yemi Osinbajo ya nada bayan sauke Daura shi ne Mathew Seiyefa, ya yi kwanaki a ofis daga Agusta zuwa Satumba a 2018.
9. Yusuf Magaji Bichi
Yusuf Magaji Bichi yana cikin shugabannin da suka fi dadewa a ofis a tarihin DSS, ya yi kusan shekaru shida daga Satumban na 2018 zuwa 2024.
10. Adeola Oluwatosin Ajayi ya karbi DSS
Da shugaba Bola Tinubu ya yi waje da Yusuf Bichi, wanda ya nada ya zama shugaban na DSS shi ne Adeola Oluwatosin Ajayi daga Kudu maso yamma.
Labari ya zo cewa Shugaban kasa ya amince da nadin Adeola Oluwatosin Ajayi a matsayin sabon shugaban DSS ne tare da sabon shugaban NIA.
Asali: Legit.ng