Tarihin sabon Shugaban Hukumar tsaro na DSS Yusuf Bichi

Tarihin sabon Shugaban Hukumar tsaro na DSS Yusuf Bichi

A jiya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sabon Shugaban Hukumar tsaro na DSS. Buhari ya nada Yusuf Magaji Bichi a matsayin wanda zai ja ragamar Hukumar bayan korar Lawal Daura daga aiki da aka yi kwanaki.

Tarihin sabon Shugaban Hukumar tsaro na DSS Yusuf Bichi
An nada Yusuf Bichi a matsayin Shugaban Hukumar DSS
Asali: Depositphotos

Mun kawo maku takaitaccen tarihin sabon Shugaban na Hukumar tsaron kasar.

1. Karatu

Yusuf Bichi Ya fara karatu ne a wata Makarantar Sakandare da ke Garin Danbatta a Kano. Bayan nan Bichi ya tafi kwalejin sharer fage ta Zariya har kuma ya samu shiga Jami’ar Ahmadu Bello inda ya karanci ilmi harkar siyasa.

2. Inda ya fara aiki

Sabon Shugaban DSS din ya soma aiki ne a matsayin Jami’in tsaro a gidan Gwamnatin Jihar Kano kafin ya koma Hukumar tsaro na NSO shekaru kusan 30 da su ka wuce. NSO ce dai ta hafi DSS a lokacin mulkin Janar Ibrahim Babangida.

KU KARANTA: Ana neman Kotun ta daure Bukola Saraki a kurkuku

3. Kwarewa a wajen aiki

Yusuf Magaji Bichi yayi karatu a wurare da dama wanda daga ciki har da Ingila. Bichi yayi kwas na harkar tsaro da sanin aiki a kwalejin tsaro ta Birtaniya da kuma wasu kwas kan binciken tsaro da kwantar da tarzoma a cikin gida Najeriya.

4. Matsayi a Hukumar DSS

Daga shekarar da ya fara aiki a matsayin Jami’in tsaro na Hukumar DSS, Bichi yayi aiki har ya kai Darekta a Makarantar koyon sirrin yaki na Najeriya. Bichi ya kuma rike Darekta a kwalejin tsaro na Hukumar DSS ban da matsayi da ya rike a sama da wurare 3 dabam-dabam na Hukumar. Bichi ya kuma rike Darektan DSS a Jihohin Jigawa, Neja, Sokoto da kuma Abiya.

5. Lokacin soma aiki

Bichi zai shiga ofis ne a yau 14 ga wannan Watan inda zai karbi shugabanci daga hannun Abokin aikin sa Matthew Seiyeifa wanda aka nada rikon kwarya bayan an sallami Lawal Daura. Bichi yana da aure da Iyali inji fadar Shugaban kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng