Dogs: Sheikh Daurawa Ya Tunawa Matasa Alkawarin da Suka Dauka idan Ta Fashe

Dogs: Sheikh Daurawa Ya Tunawa Matasa Alkawarin da Suka Dauka idan Ta Fashe

  • Aminu Ibrahim Daurawa ya samu labarin ‘Yan Crypto sun samu kudi amma babu wani wanda ya tuna da shi
  • Wasu sun rika yi wa babban malamin addinin musuluncin alkawura iri-iri a baya kafin Dogs ta fashe a kasuwa
  • A cikin raha, Sheikh Aminu Daurawa ya tuna masu cewa kyawun alkawari cikawa tun da an samu kudi

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi magana yayin da aka ji labarai suna yawo cewa an samu kudi da crypto kwanan nan.

Mutane musamman matasa da ke harkar cypto suna cike da farin ciki a sanadiyyar kwandalar Dogs da Mista Pavel Durov ya kirkiro.

Aminu Daurawa
'Yan Crypto sun samu kudi sun manta da Aminu Daurawa Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Asali: Facebook

Aminu Ibrahim Daurawa ya tabo 'yan Crypto

Kara karanta wannan

Kano: Abba ya ja kunnen jami’ai, an karyata zancen saida filin masallacin idi

Ganin an sami kudi, a shafinsa na Facebook, babban malamin addinin musuluncin ya ce ya ji shiru bayan jama’a sun yi masa alkawari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ina waɗanda suka yiwa Malam Alƙawura cewa idan ta fashe....?
“Ya ake ciki,? malam fa yaji shiru.”

- Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

An yi Sheikh Daurawa alkawuran iska

A wasu karatuttukansa a baya, shugaban na hukumar Hisbah ya shaida cewa mutane sun ce za su tuna da shi idan ta fashe.

Rahoton Nairametrics ya bayyana cewa Dogs ya shiga kafar Binance, Bybit da OKX ana ta cinikinsa kuma ya tashi sosai a kasuwa.

Akwai wadanda suka yi alkawarin gina masallatai ko gyara wuraren ibada da dai sauran nau’ukun taimakon addini da kudin.

Za a sayawa Daurawa jirgi da kudin Pi

Abba Labour ya fadawa malamin cewa za su saya masa jirage biyu masu saukar ungulu idan ta sake fashewa.

Kara karanta wannan

Jigawa: Mai shayi ya lakaɗawa matashi duka har lahira kan ɓatan Indomi da Burodi

A cewar Muhammad Usman Kargi, Sheikh Daurawa ya yi addu’a sosai kafin ta fashe.

Shi kuwa Yasir Ibn Sani cewa ya yi bai kamata a ba malamin musulunci kudin crypton da aka radawa sunan kare ba.

A cika alkawari kawai a cewar Yusuf Abubakar Attah da Nura Shehu Yelwa tun da mutane sun samu kudi.

Sulaiman Adam Rano ya ce sai dai malam ya yi hakuri domin bashi suka biya wannan karo, a jira sai lokacin da Pi ta fashe tukun.

Musa Kyari da manya a harkar irinsu Muhd King Cash ba su yi rowa ba, har suna cewa za su ziyarci Malam Daurawa a ofishin Hisbah.

Kuna da labari malaman musulunci kamar Sheikh Jamilu Zarewa suna ganin akwai magana a dukiyar Crypto saboda sabawa addini.

Kafin Sheikh Jamilu Zarewa ya ba da fatawa, sai da ya yi dogon nazari inda ya nemi jin ta bakin wadanda suka san harkar da kyau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng