Gobara Ta Babbake Rukunin Gidajen Ma’aikatan Gwamnati, Bayanai Sun Fito

Gobara Ta Babbake Rukunin Gidajen Ma’aikatan Gwamnati, Bayanai Sun Fito

  • Rahotanni sun bayyana cewa gobara ta babbake rukunin gidajen ma'aikatan gwamnatin jihar Legas da ke Odunsanmi a Ogba
  • An tattaro cewa gobarar ta babbake wani gida mai hawa har uku da wani gida mai dakuna biyu da sauran wasu gidajen a Legas
  • Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Legas, LASEMA ta ce an samu nasarar shawo kan wutar, amma an yi asarar miliyoyi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - An samu tashin gobara a rukunin gidajen ma'aikatan gwamnatin jihar Legas da ke Odunsanmi, kan titin WEMPCO a unguwar Ogba.

Rahotanni sun ce gobarar ta tashi ne ne da misalin karfe 2:20 na safiyar yau Juma'a, 30 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Malaman addini sun samo dabara, an nemowa Tinubu hanyoyin rage tsadar abinci

LASEMA ta yi magana kan gobara da ta tashi a rukunin gidajen ma'aikatan gwamnati
Legas: Rukunin gidajen ma'aikatan gwamnati ya kama da wuta. Hoto: @LagosRescue
Asali: Twitter

Gobara ta kone gidajen ma'aikata

Channels TV ta tattaro cewa gobarar ta babbake wani gida mai hawa uku da gida mai dakuna biyu da ke a Flat 5 na Block 21 da sauran wasu gidajen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Binciken farko da hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas, LASEMA ta gudanar, ya nuna cewa gobarar ta tashi ne sanadin matsalar wutar lantarki a dakin yara.

Babban sakataren LASEMA, Dakta Femi Oke-Osanyitolu, ya ce gobarar ta lalata dakin kwanan yaran gaba daya, wanda ya yi sanadiyar asarar dukiyoyi na miliyoyin Naira.

An yi asarar rayuka a gobarar?

Jaridar Guardian ta ruwaito Dakta Femi ya kara da cewa:

“Kai daukin gaggawa na hadin gwiwa da hukumomin LRT, NPF, LSFRS suka yi ya taimaka wajen shawo kan gobarar tare da dakile yaduwarta.
“Abin farin ciki shi ne gobarar da ta tashi ba ta jawo asarar rai ko jikkata mazauna gidajen ba.

Kara karanta wannan

Kwalliya ta zo da gardama: Budurwa ta sheka lahira a wajen tiyatar karin mazaunai

"Haka kuma, an wayar da kan wadanda abin ya shafa da sauran mutanen da ke zama a rukunin gidajen kan muhimmancin kiyaye amfani da na'urorin lantarki."

Gobara ta babbake kasuwar Legas

A wani labarin, mun ruwaito cewa mummunar gobara ta babbake kasuwar Balogun, daya daga cikin manyan kasuwannin jihar Legas.

Ibrahim Farinloye, shugaban hukumar NEMA a shiyyar kudu maso yamma, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce shaguna sun kone.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.