Abin da Ya Kawo Cikas ga Shirin Kamfanin BUA na Sauke Farashin Siminti zuwa N3500

Abin da Ya Kawo Cikas ga Shirin Kamfanin BUA na Sauke Farashin Siminti zuwa N3500

  • Shugaban kamfanin BUA, AbdulSamad Rabiu ya bayyana cewa ya yi iya kokarinsa domin sauke farashin siminti
  • AbdulSamad ya ce sai da kamfaninsa ya sayar da tan miliyan daya na siminti ga dillalai a kasa da N3,500 domin a samu sauki
  • Sai dai ya nuna takaicinsa kan yadda ya ce dillalan sun ki karya simintin inda har wasu ke sayar da shi N7000 ko sama da haka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kamfanin simintin BUA, ya zargi ‘yan kasuwa, musamman diloli da zama silar tsadar da siminti ya yi a fadin kasar nan.

Shugaban kamfanin simintin BUA, AbdulSamad Rabiu ya bayyana hakan a babban taron kamfanin karo na takwas a Abuja, ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Dogs: Sheikh Daurawa ya tunawa matasa alkawarin da suka dauka idan ta fashe

BUA ya yi magana kan tsadar farashin siminti a Najeriya
BUA ya bayyana abin da ya jawo siminti ke tsada a Najeriya. Hoto: @BUACement
Asali: UGC

Tsadar siminti: Kamfanin BUA ya magantu

A cewar rahoton jaridar The Nation, AbdulSamad ya ce dillalan ne ke kawo cikas ga dukkanin wani shirinsa na sauke farashin siminti.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

AbdulSamad ya bayyana cewa kamfanin simintin BUA ya sanya farashin buhun siminti mai nauyin 50kg a kan N3,500, matakin da zai saukaka simintin ga masu amfani da shi.

Sai dai shugaban kamfanin na BUA ya ce wannan rage farashin bai kai ga mutane gama gari ba da 'yan kasuwar suka ki sauke farashinsu.

BUA ya sayar da siminti N3500

Da yake karin haske a wurin taron, BUA ya ce kamfaninsa ya sayar da sama da tan miliyan daya na siminti ga dillalan a kasa da N3,500 kan kowane buhu, inji rahoton Channels TV.

“Mun sayar da siminti ga dillalai kan farashin da za su iya sayar da shi kan N3,500 amma burinsu na samun riba mai yawa ya sa suka rika sayar da shi sama da N7,000."

Kara karanta wannan

Kano: Abba ya ja kunnen jami’ai, an karyata zancen saida filin masallacin idi

AbdulSamad ya yi takaici, yana mai nuni da cewa son zuciya na wadannan dillalai da faduwar darajar Naira ne suka jawo tashin farashin da ake gani a kasuwa.

BUA ya karya farashin siminti

A wani labarin mun ruwaito cewa kamfanin simintin BUA, ya sanar da sauke farashin buhun siminti zuwa N3,500 domin saukakawa 'yan kasar kan halin da ake ciki.

A cewar kamfanin, wannan wani mataki ne na saukaka wa al'ummar Najeriya a kokarinsu na yin gine-gine kuma sabon farashin zai fara aiki daga 2 ga Oktobar 2023.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.