Yajin Aiki: Gwamnatin Tinubu Ta Kakaba Tsarin ba Aiki ba Biyan Albashi, an Samu Bayanai
- Gwamnatin tarayya ta kakaba tsarin “ba aiki, babu albashi” a kan kungiyar likitocin NARD kan yajin aikin da ta shiga
- Ma'aikatar lafiya da walwalar al'umma ta bayyana cewa babu likitan da zai karbi albashi na tsawon kwanakin yajin aikin
- Likitocin da ke neman kwarewar aiki a karkashin kungiyar NARD sun shiga yajin aikin gargadin ne a dalilin dace wata likita
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ma’aikatar lafiya da jin dadin jama’a ta tarayya ta kakaba tsarin “ba aiki, babu albashi” a kan kungiyar likitocin NARD kan yajin aikin gargadi da ta shiga kwanan nan.
NARD, kungiya ce ta likitoci masu son sanin makamar aiki a manyan asibitocin Najeriya.
Likitoci sun fusata gwamnatin tarayya
Ma’aikatar lafiyar ta bakin kakakinta, Ado Bako, ta bayyana rashin jin dadinta game da matakin NARD na shiga yajin aikin gargadin, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ma’aikatar ta ce likitocin masu neman kwarewar aiki sun shiga yajin aikin ba tare da sun yi la’akari da duk wata tattaunawa da kuma rokon da gwamnatin tarayya ta yi ba.
Sanarwar ta ce ma'aikatar ta yi takaicin wannan yajin aiki da likitocin suka shiga, tana mai cewa tattaunawa ya fi fa'ida wajen warware dukkanin matsalolin kungiyar.
Gwamnati ta kakaba tsarin hana albashi
Jaridar The Punch ta ruwaito Ado Bako, ya bayyana cewa ma'aikatar lafiya da walwalar jama'a ta yanke shawarar cewa:
"A bisa amfani da dokokin aiki, gwamnatin tarayya za ta kakaba tsarin "babu aiki-babu albashi" na tsawon kwanaki da aka gudanar da yajin aikin.
"Ba a dauki wannan matakin domin nuna rashin damuwa da matsalolin likitocinmu ba, sai dai domin mu tabbatar da cewa ba a gurgunta ayyukan da suka jibinci kiwon lafiyar jama'a ba."
Likitoci sun shiga yajin aiki
Tun da fari, mun ruwaito cewa likitoci karkashin kungiyar NARD sun tsunduma yajin aikin gargadi bayan da 'yan bindiga suka yi garkuwa da Dakta Ganiyat Papoola.
Kungiyar likitocin masu son sanin makamar aiki sun shiga yajin aikin ne bayan da suka yi zargin cewa gwamnatin tarayya ta ki sanya baki domin a kubutar da babbar likitar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng