Gwamna a Arewa Ya Shirya Zaben Ciyamomi, Ya Ayyana Juma’a a Matsayin Ranar Hutu
- Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya ayyana ranar 30 ga Agusta a matsayin ranar hutu ga ma'aikata domin tunkarar zaben ciyamomi
- Wata sanarwa daga kwamishinan fansho da horarwa na jihar, Hon. Auwal Manu-Dogondaji ta ce ranar Asabar 31 ga Agusta za a yi zaben
- Gwamnatin Kebbi ta yi kira ga ma’aikata da daukacin al’umma da su fito kwansu da kwarkwata a ranar zaben kananan hukumomin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi ta ayyana ranar Juma’a, 30 ga Agusta a matsayin ranar hutu domin jama’a su shirya tunkarar zaben kananan hukumomin da za a yi ranar Asabar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga kwamishinan fansho da horarwa Hon. Auwal Manu-Dogondaji, wanda ya rabawa manema labarai a Birnin Kebbi ranar Alhamis.
An ba da hutun zaben ciyamomi a Kebbi
Sanarwar wadda aka wallafa a shafin gwamnatin Kebbi na X, ta ruwaito kwamishinan na cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Mai girma gwamna, Kwamared Dakta Nasir Idris, Kauran Gwandu ya amince da gobe Juma’a 30 ga Agusta, 2024 a matsayin ranar hutu."
“An ba da hutun ne domin baiwa masu zabe damar shirya kansu a zaben kananan hukumomi da ke tafe, wanda za a gudanar a ranar Asabar, 31 ga Agusta, 2024."
Gwamnati ta gargadi masu zabe
Hon. Auwal Manu-Dogondaji ya ce gwamnatin jihar ta yanke shawarar ba al'umma damar shiryawa domin tunkarar wannan babbar rana ta kada kuri'arsu.
Don haka gwamnati ta yi kira ga ma’aikatan gwamnati da kuma daukacin al’umma da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin zabar shugabannin da za su jagorance su.
A yayin da yake kira ga jama’a da su ci gaba da rungumar zaman lafiyan da ake samu a fadin jihar, kwamishinan ya nemi al’umma da su nuna dattako yayin zaben da kuma bayansa.
Sanarwa daga hukumar zaben jihar Kebbi
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar zaben jihar Kebbi (KESIEC) ta bayyana ranar da za a gudanar da zaben kananan hukumomi 21 na jihar.
Hukumar KESIEC ta bayyana cewa za ta gudanar da zaben ciyamomin a ranar 31 ga watan Agusta, bayan samun amincewar gwamnan jihar, Dakta Nasir Idris.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng