Gwamnan Katsina Ya Nunawa Ƴan Bindiga Yatsa, Ya Yi Sallah a Titin da Ake Sace Mutane

Gwamnan Katsina Ya Nunawa Ƴan Bindiga Yatsa, Ya Yi Sallah a Titin da Ake Sace Mutane

  • Gwamnan Katsina, Mallam Dikko Umaru Radda ya sake nuna bajintarsa da kuma jaddada kurinsa na yaki da ta'addanci a jiharsa
  • An ruwaito cewa gwamnan ya bi ta kan hanyar Kankara zuwa Sheme, kuma har ya yi Sallah kan hanyar duk da fargabar da ake yi
  • An ce an rufe hanyar Sheme zuwa Kankara saboda hare-haren 'yan bindiga da suka yadda matafiya da kuma mazauna yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - Gwamna Dikko Umaru Radda ya yi wani abun bajinta a ranar Alhamis, 29 ga watan Agusta a lokacin da ya ke hanyar komawa Katsina daga Faskari.

An ce gwamnan na jihar Katsina ya ziyarci karamar hukumar Faskari domin ta'aziyyar mahaifiyar kwamishinansa, Hon. Hamza Sule Faskari.

Kara karanta wannan

Kwalliya ta zo da gardama: Budurwa ta sheka lahira a wajen tiyatar karin mazaunai

Gwamnan Katsina ya yi Sallah a kan hanyar da 'yan bindiga suka addaba
Gwamnan Katsina ya bi kan hanyar da aka rufe saboda hare-haren 'yan bindiga. Hoto: @Miqdad_Jnr
Asali: Twitter

Hatsarin hanyar Kankara-Sheme a Katsina

Mai tallafawa Dikko Radda ta fuskar kafofin sada zumunta, Isah Miqdad ya wallafa a shafinsa na X cewa gwamnan ya yi sallar Azuhur a titin Sheme zuwa Kankara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga duk wanda ya san titin Sheme zuwa Kankara, ya san cewa hanya ce mai matukar hatsari ga matafiya, wadda a karshe aka hana mutane binta, kamar yadda rahoto ya nuna.

Hanyar Kankara zuwa Sheme ta zama tamkar 'Kadarkon Kimba,' ma'ana hanyar da 'yan bindiga ke cin karensu ba babbaka a duk lokacin da mutane suka bi ta.

Gwamnan Katsina ya yi sallah a mugun titi

Sai dai, kamar yadda hadimin gwamnan ya bayyana, duk da irin hatsin da hanyar ta ke da shi, hakan bai hana Gwamna Dikko Radda tsayawa ya yi Sallah a kanta ba.

Isah Miqdad ya bayyana cewa:

Kara karanta wannan

Abba ya samu giɓi ana shirin zabe, shugabannin Kwankwasiyya sun koma APC

"Gwamna Malam Dikko Umaru Radda da tawagarsa sun gudanar da Sallar Zuhur a kan hanyar Kankara zuwa Sheme.
"Sun tsaya yin Sallah a hanyar ne a wata ziyara da suka kai karamar hukumar Faskari domin yi wa kwamishinan muhalli Hon. Hamza Sule ta'aziyyar rasuwar mahaifiyarsa.
An rufe hanyar ne sakamakon ayyukan ‘yan bindiga da suka addabi yankin, kuma gwamnan ya jaddada kudurinsa na dawo da zaman lafiya da tsaro a wadannan yankuna."

Duba hotunan a kasa:

"Hanyar dawo da tsaro" - Gwamnan Katsina

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya yi magana kan hanyar magance matsalar rashin tsaro da ta addabi kasar nan.

A cewar gwamnan, idan har ana son magance matsalar tsaro, to akwai bukatar magance matsalar iyakokin kasar tare da kawo karshen cin hanci da rashawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.