Dakile matsalar tsaro: Jerin sabbin dokoki 10 da Masari ya kafa a jihar Katsina
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya kafa wasu sabbin dokoki goma domin shawo kan matsalar tsaron da ta addabi jihar sama da shekaru biyu yanzu.
A takardar da gwamnan da kansa ya rattafa hannu mai kwanar wata 30 ga Agusta, 2021 kuma Legit ta samu, gwamnan ya bada umurnin kulle wasu hanyoyi da kuma safarar wasu kayayyaki.
Hakazalika Gwamna Masari ya dawo da dokar hana yawo da babura da a daidaita sahu da dare.
Gwamnan yace wadannan dokoki zasu fara aiki ne daga ranar Talata, 31 ga watan Agusta.
Ga jerin dokokin busa sanarwar da gwamnatin jihar tayi:
1. Rufe hanyar Jibia-Gurbin har zuwa lokacin da hali yayi
2. Rufe titin Kankara-Sheme ga masu motocin haya
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
3. Haramtawa manyan motoci daukan itace daga daji
4. An dakatad da sayar da dabbobi a kananan hukumomi 14 (Jibia, Batsari, Sfana, DanMusa, Kankara, Malumfashi, Charanci, Ma'adua, Kafur, Faskari, Sabuwa, Baure, Dutsinma, da Kaita.)
5. An haramta fitar da dabbobi daga jihar Katsina zuwa wata jiha a Najeriya
6. An haramta daukar mutum 3 kan babur kuma sama da mutum uku kan Keke Napep
7. An haramta sayar da baburan da ba sabbi ba a kasuwar Charanci
8. An dawo da dokar hana amfani da babura da Keke Napep daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe
9. An haramta sayarwa masu jarkuna man fetur a gidajen mai
10. Gidajen Mai biyu kacal aka amince su sayar da mai na fiye da N5000 a kananan hukumomi 14 (Jibia, Batsari, Sfana, DanMusa, Kankara, Malumfashi, Charanci, Ma'adua, Kafur, Faskari, Sabuwa, Baure, Dutsinma, da Kaita.)
Wannan ra'ayin ka ne: FG ta yi wa Masari martani kan cewa mutane su kare kansu daga ƴan bindiga
A bangare guda, gwamnatin tarayya ta yi watsi da kiran da Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina da takwararsa na Jihar Benue, Samuel Ortom, da wasu kungiyoyi da mutane suka yi na cewa mutane su kare kansu daga 'yan bindiga.
Ministan Harkokin 'Yan sanda, Mohammed Dingyadi, yayin jawabin shekara-shekara na ma'aikatarsa karo na biyu a hedkwatar yan sanda a Abuja ya ce gwamnati bata goyon bayan mutane su dauki makamai da kansu.
Asali: Legit.ng