Bidiyon Yan Ta'adda: Tsohon Hadimin Shugaba Buhari Ya Fadi Illar Tik Tok a Najeriya

Bidiyon Yan Ta'adda: Tsohon Hadimin Shugaba Buhari Ya Fadi Illar Tik Tok a Najeriya

  • Tsohon hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya bayyana cewa rashin amfanin shafin tiktok ya fi amfaninsa yawa a kasar nan
  • Bashir Ahmad ya bayyana haka ne bayan yawaitar bidiyon masu garkuwa da mutane rike da kudin fansa da su ka karba daga jama'a
  • Tsohon hadimin ya bayyana cewa akwai bukatar hukumomin kasar nan su sanya sharudda da dokar amfani da shafin a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Bashir Ahmad, tsohon hadimin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana takaicin yadda yan ta'adda ke cin karensu babu babbaka a shafin Tiktok.

Wannan na zuwa ne bayan bullar jerin bidiyon wasu 'yan ta'adda su na nuna kudin fansar da su ka karba.

Kara karanta wannan

Kasuwancin Arewa zai habaka, tashar tsandaurin Kebbi ta bude ofishi a Kano

Bashir
Tsohon hadimin Buhari ya nemi a sa dokoki kan shafin tiktok Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na X cewa lamarin yadda miyagu ke baje hajarsu a shafin tiktok na nuni da cewa akwai matsala babba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Akwai bukatar sa doka kan tiktok," Bashir Ahmaad

Jaridar Leadership ta bayyana cewa tsohon hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya ce akwai bukatar gwamnati ta sa doka da za ta rika sa ido kan abubuwan da ake wallafawa a shafin tiktok.

Ya bayyana haka ne bayan an gano yan ta'adda su na wallafa bidiyon kudin fansa, da kawunansu rike da makai a shafin tiktok.

Tiktok na jawo matsala a kasa?

Bashir Ahmad ya bayyana cewa shafin tiktok na jawo matsaloli ga kasar nan, domin ya na ba miyagu damar kara bayyana mugun aikinsu.

Ya ce shafin ya na kara ba yan ta'adda damar yada mugun nufinsu a cikin jama'a, yayin da su ke cusawa jama'a mummunan ra'ayi.

Kara karanta wannan

Sunayen gwamnonin Arewa da ake zargin sun kitsa zanga zangar adawa da Tinubu, Rahoto

'Yan ta'adda na baje koli a tiktok

A wani labarin kun ji cewa wasu daga cikin masu garkuwa da mutane sun fara baje kolin muguwar sana'arsu a shafin tiktok, yayin da su ke cigaba da kai farmaki garuruwan kasar nan.

Miyagun sun fara tallata kudin fansa da su ke karba a shafin tiktok, amma tsohon ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Farfesa Isa Ibrahim Pantami ya ce za a iya magance matsalar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.