Digiri Dan Kwatano: Gwamnati Ta Lissafa Jami’o’in Benin, Togo da Ta Amince da Su
- Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ce akalla dalibai 21,600 ne suka mallaki takardun digiri na bogi daga jami'o'in Benin da Togo
- Binciken da Najeriyar ke yi na da nufin magance yawaitar digirin bogi da ya girgiza harkar ilimin kasar biyo bayan rahoton kwakwaf
- Duk da haka, an bayyana cewa ba dukkanin daliban Najeriya a Jamhuriyar Benin da Togo ne ke karatu a jami'o'in da ba a amince da su ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa jami’o’i biyar ne kacal a jamhuriyar Benin da uku a Togo aka amince da su a hukumance.
Gwamnatin ta ce wadannan jami'o'in ne kadai aka amince 'yan Najeriya su je su yi karatu a ciki domin samun shaidar kammala digiri.
Ministan ilimi, Tahir Mamman ne ya bayyana hakan a wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi, 25 ga watan Agusta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An bankado badakalar digirin bogi
Dangane da dakatar da karbar digiri daga Jamhuriyar Benin da Togo bayan badakalar digirin bogi da aka bankado, Mamman ya ce matsalar hadari ce ga kasar.
Tahir Mamman ya jaddada buƙatar kiyaye mutuncin ilimi tare da yin alƙwarin haɗa gwiwa da hukumomin da abin ya shafa domin dawo da martabar tsarin.
Mun ruwaito ministan ya sha alwashin tsaftace fannin ilimi a Najeriya yana mai nuna rashin jin daɗinsa da irin abubuwan da aka bankaɗo a lokacin binciken digirin bogi.
Jami'o'in da aka amince da su
Duba jerin jami'o'in Benin da Togo da ke da lasisin yin digiri a ƙasa:
- Jami'ar Abomey-Calavi, Jamhuriyar Benin
- Jami'ar Parakou, Jamhuriyar Benin
- Jami'ar UNSTIM Abomey
- Jami'ar noma ta kasa da ke Jamhuriyar Benin
- Jami'ar ADC da ke Jamhuriyar Benin
- Jami'ar Lomé, Togo
- Jami'ar Kara, Togo
- Jami'ar Katolika ta Yammacin Afrika, Lome, Togo
Duba cikakken jerin a nan kasa da @Theumar_audu ya wallafa a shafinsa na X:
Jami'o'i 9 da ake bincike a Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar kula da jami'o'i ta kasa (NUC) ta fara gudanar da bincike kan wasu jami'o'in Najeriya tara da ake bincikarsu kan badakalar digirin bogi.
A yayin da hukumar NUC ta lissafa jami'o'in ta kuma ce dukkanin daliban kasar da suka samu digiri daga jami'o'in to ya kuka da kansa har zuwa lokacin da za ta kammala bincike.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng