Atiku Ya Bankado Zargin Yadda Tinubu Ke Son Amfani da Kuɗin Tallafin Mai a Zaben 2027

Atiku Ya Bankado Zargin Yadda Tinubu Ke Son Amfani da Kuɗin Tallafin Mai a Zaben 2027

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya sake magana cewa gwamnatin Bola Tinubu ta dawo da tallafin mai
  • A maganar da ya yi a wannan karon, Atiku Abubakar ya ce Bola Tinubu na son yin amfani da kuɗin tallafin mai domin zaben 2027
  • Haka zalika Wazirin na Adamawa ya zargi Mai girma Tinubu ta shirin kawo cikas da gangan ga matatar Dangote da ke jihar Legas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa a PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ya yi kira ga Bola Tinubu kan dawo da tallafin man fetur.

Atiku Abubakar ya ce ya kamata shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi halin maza wajen fadawa yan Najeriya cewa ya dawo da tallafin mai maimakon boye boye da yake.

Kara karanta wannan

2027: Tinubu ya nemo hanyar shawo kan yan Arewa, an fadi dabarun da ya shirya

Atiku da Tinubu
Atiku ya fito da bayanai kan tallafin mai da zaben 2027. Hoto: Atiku Abubakar|Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa Atiku Abubakar ya ce tallafin da ake biya a yanzu ya ninka wanda ake biya a baya sosai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kudin tallafi mai a zaben 2027

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin tarayya da boye gaskiya kan dawo da tallafin man fetur a kan shirin zaben 2027.

The Guardin ta wallafa cewa Atiku Abubakar ya ce Bola Ahmed Tinubu yana son yin amfani da kuɗin tallafin mai ne domin tara kudin yakin neman zaben 2027.

Atiku ya bukaci Tinubu ya yi halin maza

Atiku Abubakar ya ce abin takaici ne yadda Bola Ahmed Tinubu ya gaza yin halin maza ya fadawa yan Najeriya gaskiya kan maido tallafin man fetur.

Ya ce duk da kamfanin NNPCL ya fito ƙarara ya nuna cewa yana bin gwamnatin tarayya kudin tallafin mai N7.8trn amma Tinubu ya noke kan cire tallafin.

Kara karanta wannan

Ana cikin badakalar kwangila, Gwamna Abba Gida Gida ya rikice da ayyuka a Kano

Magana kan wahalar man fetur

Atiku Abubakar ya kara da cewa abin takaici ne matuka kan yadda aka shiga wahalar mai duk da tsadarsa a Najeriya duk da kudin da ake kashewa a bayan fage da sunan tallafi.

Haka zalika, Atiku ya ce bai kamata gwamnatin tarayya ta rika cin dunduniyar Matatar Dangote ba duba da yadda ake wahalar mai a Najeriya.

Jigon APC ya ba Tinubu shawara

A wani rahoton, kun ji cewa wani jigo a jam'iyyar APC, Olatunbosun Oyintiloye ya koka kan matsalar da yan Najeriya ke ciki a yanzu.

An ruwaito cewa Mista Olatunbosun Oyintiloye ya ce lokaci ya yi da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai magance matsalolin da suka addabi Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng