El Rufai Ya Shiryawa Arewa Gagarumin Taron Fasaha a Kano, Ya Gayyato Sarki Sanusi II
- Malam Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan Kaduna zai gudanar da wani babban taro a Arewacin Najeriya kan fasaha da kere-kere
- An ce Malam Nasir El-Rufai ya gayyaci manyan masu fasaha, 'yan kasuwa, masu kirkire-kirkire da masu zuba jari zuwa wajen taron
- Hakazalika, ana sa ran tsohon gwamnan zai kaddamar da babban kamfanin fasaha na Afri Ventures wanda ya kafa da kansa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya shirya sauya fannin fasaha a Arewacin Najeriya ta hanyar kaddamar da kamfaninsa mai suna Afri Ventures Capital.
Nasir El-Rufai na shirin hada kan masu sha’awar fasahar kere-kere, ‘yan kasuwa, masu kirkire-kirkire, masu zuba jari, da masu tsara manufofi a fadin Afrika.
An shirya taron Arewa TechFest
A cewar wani rahoto na Daily Trust, tsohon gwamnan na kokarin tattaro kan wadannan masu fasaha domin zuba jari mai yawa a fannin fasaha a yankin Arewacin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akuma ce masu zuba jari da masu fasahar za su halarci kaddamar da Arewa TechFest 2024, wani babban taro kan fasaha da za a gudanar na farko irinsa a Arewa.
Taron wanda aka shirya yinsa a Kano daga ranar 25 zuwa 26 ga watan Satumba, ya samu cikakken goyon bayan gwamnatin Kano da Gwamna Abba Yusuf Kabir, inji rahoton BusinessDay.
Malam Nasir El-Rufai ya ce Arewa Tech Fest wani gagarumin taro ne da ke nuna irin karfin da Arewacin Najeriya ke da shi a fannin fasaha da kirkire-kirkire
El-Rufai ya gayyaci sarkin Kano
Wannan yunƙurin yana da nufin fito da sababbin ci gaban fasaha da aka samu, da kuma harkar kirkire-kirkire, kasuwanci, wanda zai kawo ci gaban tattalin arzikin Arewa da Najeriya baki daya.
Manyan mutanen da za su yi jawabi a wajen taron sun hada da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II; Shugaban bankin Afreximbank da Benedict Oramah.
Sauran sun hada da; Babban jami’in hukumar kula da harkokin kudi na Afirka, Sumaila Zubairu da kuma wacce ta kafa Outsource Global, Amal Hassan.
El-Rufai ya je gidan Atiku
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan Kaduna ya jagoranci wata tawaga zuwa gidan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
An ce tsohon gwamnan na Kaduna ya jagoranci tawagar ne domin neman auren 'yar Atiku, Hafsat Atiku Abubakar ga iyalan Kashim Imam.
Asali: Legit.ng