Masu fasahar kere-kere 300 ne suka hallara a bikin baje-kolin masu kananan sana’oi da jari a Kaduna

Masu fasahar kere-kere 300 ne suka hallara a bikin baje-kolin masu kananan sana’oi da jari a Kaduna

Rahotanni sun awo cewa masu fasahar kere-kere 300 daga jihohi hudu (Akwa Ibom, Enugu, Gombe fa Kaduna) ne a jiya Alhamis, 4 ga watan Afrilu suka hallara a bikin baje-kolin masu kananan sana’oi da jari a Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa an kafa shirin ne domin samar da ayyukan yi ga matasa.

Yayin da yake magana a bikin bude taron mai taken ‘Breaking Convention, Sparking Innovation’, babban Darekta kuma shugaban hukuman, Dr. Dikko Umaru Radda, yace shirin zai tabbatar da gano fasahar da ke boye da kuma baje kwanjin sani a fannin ado, zane-zane da kuma saka.

Masu fasahar kere-kere 300 ne suka hallara a bikin baje-kolin masu kananan sana’oi da jari a Kaduna
Masu fasahar kere-kere 300 ne suka hallara a bikin baje-kolin masu kananan sana’oi da jari a Kaduna
Asali: Facebook

Ya ayyana cewa shirin zai samar da hanyoyin arziki da dogaro ga kai, wanda hakan zai rage yawan talauci tsakanin matasa.

KU KARANTA KUMA: Ganduje zai rushe majalisarsa a 29 ga watan Mayu, za a yi wa sabbin shiga gwajin kwaya

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa wasu matasan manoma a Damaturu sun bukaci zabeben gwamnan jihar, Mai Mala Buni ya fito da tsare-tsare na inganta ayyukan noma da fadada shi domin matasan su samu damar yin noma a daminan bana.

Mai magana da yawun kungiyar, Ali Modu ne ya yi wannan rokon a hirar da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN ranar Juma'a a garin Damaturu.

Ya ce matasa da dama sun son fara noma domin su rika samun abinda za su tallafawa kansu a maimakon jiran ayyukan gwamnati.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel